Shugaba Muhammadu Buahari ya shawarci matasan kasar nan da su kudiri aniyar nada gammon daukar babban nauyin da zai hau kan su a nan gaba, wato karbar ragamar shugabancin kasar nan.
Buhari ya yi wannan bayani a jiya Juma’a, lokacin da ya karbi bakuncin ziyarar da shugabannin matasan APC na shiyyoyin kasar nan shida a Fadar Shugaban Kasa, Aso Villa, Abuja.
Ya shawarce su da su rika kallon Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasar kasa mai al’umma mabambanta, amma ba a rika yi wa kasar kallon kabilanci ko bambancin addini ba.
“Ko ku na so ko ba ku so, to wata rana ga matasa za mu damka mulki. Wasu masu wani buri za su zo muku da kabilanci, bambancin addini, amma ya kamata ku kalli Najeriya gaba dayan ta, ba wani sashe daya za ku kalla a matsayin shi ne Najeriya ba.
“Mun yi fama da yakin Basasa, wanda ya ci rayuka sama da milyan biyu na ‘yan Najeriya. Amma mun koyi darussa daga nan. Najeriya kasa day ace, don haka kada kowa ya raina mana hankali, kasa daya muke, kuma al’umma daya.”
Shiga Ta Siyasa
Buhari ya shaida musu cewa ya shiga siyasa bayan wadanda suka daure shi sun tabbatar da cewa ba shi da wani laifin satar dukiyar Najeriya.
Hakan inji shi ya faru ne bayan da aka kifar da gwamnatin sa ta soja cikin 1985. An binciki rakod din sa ya na gwamnan Arewa maso Gabas, Ministan Fetur da kuma Shugaba na mulkin soj, amma ba a same shi da laifin wawurar kudin kasar nan ba.
“Bayan da aka sake ni, ba a kama ni da wani laifi ba. Sai na fara sha’awar shiga siyasa. To dalili kenan, domin na yi wa al’umma aiki a cikin nagartar da na ke da ita. Shi ya sa na yi sha’awar yin mulki na dimokradiyya.”
Da ya ke magana a kan wannan zangon sa na biyu, Buhari ya ce zai kara zuba ido sosai wajen rashin yarda da ayyukan da ba daidai ba, zai kara jajircewa tare da gudanar da ayyukan tsare kasar nan, inganta tattalin arziki ta yadda kowa zai samu aiki tare da yaki da rashawa da cin hanci.