Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta fi kowace kasa karfin makamai wadanda ta jibge a Gabas ta Tsakiya, amma duk da haka ya ce ba za a yi yaki da Iran ba, sai dai neman a yi zaman lafiya da juna.
A jawabin da ya yi a safiyar yau Laraba a can kasar, wato dai dai karfe 6 na yamma a Najeriya, Trump ya ce “Amurka na da karfin da yq zarce na kowa, sojojin da suka saura iya yaki, makaman da suka fi balbalin bala’i da ta jibge a Gabas ta Tsakiya, amma ba za a yi yaki da Iran ba.”
Trump ya ce zaman lafiya ake fata a duniya, ba tashin hankali ba. Don haka ba ta yi amfani da karfin makamai a kan Iran ba, amma za ta ci gaba da kakaba wa kasar takunkumin tattalin arziki har sai shugabannin Iran sun daina goyon bayan abin da ya kira ta’addanci.
Haka kuma Trump ya ce ba a kashe kowa ba a harin da Iran ta kai wa sansanoni biyu na Amurka a Iraqi.
A jawabin bazata da ban-al’ajabi, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ba ta bukatar kafsa mummunan yaki da kasar Iran, ta fi son zaman lafiya da kowace kasa a duniya.
A jawabin da ya yi da yammacin yau Laraba, wanda duk duniya ta yi zaman jiran sauraren furucin sa, bayan harin ramuwar-gayya da Iran ta kai wa sojojin Amurka a sansanoni biyu a Iraqi, Trump ya bugi kirjin cewa Amurka ta na da makaman nukiliya, amma ba ta son amfani da su, ba kuma za ta yi amfani da su wajen haddasa asarar dimbin rayuka a duniya ba.
Dangane da harin da Iran ta kai na makami mai linzami a kan sojojin Amurka kuwa, Trump ya ce ba a kashe soja ko wani Ba’Amurke ko daya ba.
Ya ci gaba da cewa haka kuma, “Amurka ta fi kowace kasa dimbin arzikin man fetur a duniya. Don haka ba ta ma bukatar danyen man fetur daga Gabas ta Tsakiya.”
Da ya juya kan Iran, ya yi kakkausan bayanin cewa Iran ta karya yarjejeiyar da ta kulla da Amurka cikin 2015.
Sannan kuma ya ci gaba da bayanin yadda gwamnatin da ya gaba ta jam’iyyar Democrat ta rika bai wa Iran kudade, wadanda a karshe da su ne Iran din ta kera makaman da ta kai wa sansanonin Amurka din biyu hari a Iraqi.
Har ila yau ya tunatar da Iran cewa Amurka ta kashe babban jagoran ISIS, al-Baghady, wanda babban abokin gabar gwamnatin Iran ce, wadda Trump kira gwamnatin kama-karya.
“Amma maimakon Iran da al’ummar ta su gode wa Amurka, sai suka ci gaba da kiran, “Allah ya ruguza Amurka!”
Haka kuma ya tunatar da cewa, “ko ranar da aka kulla yarjejeniyar 2015 da Iran, al’ummar kasar sai da suka rera baitocin “Allah ya ruguza Amurka.”
Daga nan kuma ya yi kira ga manyan kasashe kamar Birtaniya, Rasha, Faransa, Chana da sauran su cewa su sani fa ya zama dole su hada kai domin su tabbatar da cewa Iran ta bi turbar zaman lafiya a duniya.
A karshe Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da tirsasa takunkumin tattalin arzikin da ta kakaba wa Iran, har sai gwamnatin da ya kira ta kama-karya ta Iran ta nabba’a, ta bi turbar zaman lafiya a duniya.
Trump Ya Gode Wa Al’ummar Iran
“A karshe ina kira ga al’ummar kasar Iran cewa su tuna fa su al’umma ce mai son ganin ta ci gaba a doron duniya. Don haka su kama turbar zaman lafiya, kamar yadda Amurka da sauran kasashen duniya ke so a ga ya wanzu a duniya. Na gode muku kwarai.”
Trump yayi wannan jawabi ya na tsakiyar Sakataren Tsaron Amurka da Babban Hafsan Hafsoshin Amurka.