A ranar Litinin Kotun Koli a Abuja ta dage zaman bayyana hukuncin kararrakin zabukan gwamnoni 7 da ta shirya bayyanawa a yau din.
Hakan dai ya faru ne kamar yadda kotun ta bayyana, saboda daya daga cikin alkalan ba shi da lafiya.
Hukuncin da aka yi niyyar bayyanawa a ya dai na kararrakin gwamnan Kano, Sokoto, Filato ne da kuma Binuwai.
A yau din dai Kotun Koli ta fara zaman ta karfe 9:02 daidai. Sai dai kuma cinkoson jama’a da hayaniya ta sa komai ya tsaya cak, har ta kai Cif Jojin Tarayya, Tanko Muhammad ficewa daga cikin kotun.
Hakan ya sa Tanko umarnin dage zaman, saboda jami’an tsaro sun kasa shawo kan cinkoson jama’a.
Alkalan su bakwai sun ce za su zauna kotun idan hayaniyar jama’a ta yi sauki.
Kafin a tashi daga kotun, sai Cif Joji Tanko ya umarci lauyan kowane gwamna cewa kada ya shigo kotu tare da sama da lauyoyi biyar, domin a samu saukin cinkoso a cikin kotun.
Daga nan ne kowane bangare ya rage lauyoyin sa zuwa biyar.
An kuma umarci kowane dan siyasa da ya je rakiyar gwamna, cewa idan babu shi a cikin mai kara ko wanda ake kara, to ya fice daga kotun.
Bayan an samu saukin cinkoso, sai lauyoyin bangaren Kano suka fara shiga, suka gabatar da kan su.
Yayin da lauyan INEC, Joseph Daudu ya mike zai gabatar da kan sa, sai Cif Jojin Najeriya, Tanko ya ce daya daga cikin alkalan da za su yanke hukunci ba shi da lafiya.
Daga nan sai duk suka yi zumbur, suka mike tsaye, domin su je su duba alkalin da aka ce ba shi da lafiya din.
Sai dai kuma Tanko bai bayyana sunan alkalin ba.
Bayan kamar minti 40, sai rajistara na kotun ya yi sanarwar cewa dan dage zaman kotun zuwa gobe Talata, 14 Ga Janairu.