DAKILE YADUWAR KANJAMAU: PEPFAR za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya

0

Kungiyar bada tallafi ta kasar Amurka PEPFAR ta bayyana cewa za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya wajen yaki da cutar Kanjamau.

Shugaban shirye-shirye na kungiyar Murphy Akpu ya sanar da haka inda ya kara da cewa PEPFAR za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya daga shekarar 2020 zuwa shekarun gaba masu zuwa.

Akpu yace PEPFAR za ta hada hannu da hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau ta kasa (NACA) domin ganin hakan ya tabbata.

“Ina kuma kira ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu da kungiyar mu domin ganin an samun nasarar dakile yaduwar cutar a Najeriya.

Akpu ya ce a madadin kungiyar PEPFAR ya yi wa gwamnatin Najeriya da hukumomin kiwon lafiya, masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da sauran mutane a kasar murnar shiga sabuwar shekara.

Idan ba a manta ba a watan Maris din shekarar 2019 hukumar NACA ta sanar cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar kanjamau a Najeriya.

Shugaban hukumar Sani Aliyu ya bayyana haka cewa bisa ga sakamakon binciken da hukumar ta gudanar a shekarar 2018.

Hukumar NACA ta gudanar da binciken ne domin sanin adadin yawan mutanen dake dauke da cututtukan Kanjamau, Hepatitis B da C a Najeriya.

Yin wannan bincike zai taimaka wa gwamnati wajen samar da kula da kuma inganta hanyoyin kawar da cutar daga kasar nan.

Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen dake dauke da cutar kuma masu shekaru 15 zuwa 49 sun kai kashi 1.4 inda daga ciki kashi 1.9 mata ne sannan kashi 0.9 maza.

Sannan adadin yawan mutanen dake dauke da cutar kuma ke samun kula dake da shekaru 15 zuwa 49 sun kashi 42.3 inda daga ciki kashi 45.3 mata ne sannan kashi 34.5 maza

Share.

game da Author