Binciken da Kungiyar Bin Diddigin Salsalar Makaman da ake Kashe-kashe da su a Duniya (CAR) ta gabatar, ya tabbatar da cewa da irin makaman da Al Qaeda ke yaki ake kashe-kashe a yankin Arewa maso Yamma a Najeriya.
Binciken ya ce irin makaman ne kungiyar Al Qaeda ke kashe-kashe da su a kasashen Mali da sauran yankunan Afrika da ke yankin sahel.
Wannan kungiya dai ta gudanar da bincike a kan kashe-kashen da ke faruwa a jihohin Zamfara, Katsna da Kaduna.
Mawallafin rahoton mai suna Mike Lewis, wanda kuma shi ne shugabannkungiyar, ya shaida wa Gidan Radiyon Faransa na RFI a ranar Laraba cewa, masu bincike sun gano wasu makaman da Al Qaeda ke kashe-kashe da su a Mopti da ke ysakiyar Mali, irin su ne ake kashe-kashe a yankunan Katsina, Zamfara da Kaduna.
Binciken ya kara da cewa dukkan makaman da bangarorin biyu ke amfani da su, duk masu dillancin su daya ne a bangarorin biyu.
Sannan rahoton ya kara da cewa ana shiga da muggan makamai na zamani daga kasar Turkiyya zuwa cikin Najeriya.
Ya ce sun yi bincike da nazarin yadda aka rika shigar da makamai ta ruwan Lagos a cikin 2014.
“Masu kai hare-hare a kasashe na samun makamai ba ma lallai sai iri daya ba, amma su na samun makaman ne daga wurin masu safarar makamai daya. Ko da kuwa makaman ba iri daya ba ne.
“Abin da wannan ke nunawa kuwa shi ne akwai wasu masu safarar makamai na musamman da aikin su kawai shi ne safarar makamai ga kungiyoyin da ke tayar da fitina a cikin kasashen Sahel.” Inji Lewis.
“Domin sau da dama a binciken da mu ka yi, an samu makamai musamman bindigogin da aka yi wa wata shaida ko alama iri daya da wadda aka yi wa wasu makaman, a wasu kasashe da ke nisa da juna.”
Rahoton ya ce akwai kuma rumbunan da aka dankare wasu makamai da ake safarar su daga kasashen Kwadebuwa da Libiya.