Shugaba Muhammadu Buhari ya roki hadin kai na Hukumar Binciken Masu Manyan Laifuka ta Ingila wajen binciken wasu ’yan Najeriya da suka boye a kasar, domin a maido su Najeriya a hukunta su.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina ya fitar ga manema labarai a jiya Litinin, ya ce Buhari ya yi wannan rokon a ganawar sa da Firayi Ministan Birtaniya, Boris Johnson a Landan.
Shugabannin kasashen biyu sun gana a kebance, yayin Taron Karfafa Jari na Birtaniya da Afrika, na 2020 da ke gudanar a Landan.
Buhari ya ce yaki da cin hanci da rashawar da ake yi a Najeriya ya na tafiyar hawainiya, sannan kuma ya na bukatar hadin kai daga hukumar yaki da rashawa ta Ingila.
Cikin wadanda suka falfala a guje suka makale a Ingila tun bayan hawan Buhari mulki cikin 2015, akwai tsohuwar Ministar Harkokin Fetur, Deizani Maduekwe da wasu da dama.
Cikin 2017 Mai Shari’a Abdul’azeez Anka ya bayar da umarnin gwamnatin tarayya ta rike naira bilyan 7.6 da ake zargin Deizani ta wawura.
Hukumar EFCC ce dai ta bankado kudaden kuma ta kwato su.
Buhari ya yi wa Johnson karin bayanin irin ci gaban da aka samu dangane da ingantawa da bunkasa Najeriya a karkashin mulkin sa.
Ya shaida masa cewa an samu bunkasar harkar noma, har ta kai a yanzu Najeriya ta na iya ciyar da kan ta shinkafa da sauran kayan nau’o’in abinci, ba tare da an shigo da su daga kasashen waje ba.
Batun ta’addanci kuwa, Buhari ya ce tsaro na kara inganta sosai a yanzu, tare da samun nasarar kwance wa matasa da dama mummunar akidar da Boko Haram wadda a baya suka cusa wa kan su a cikin kwakwalwar su.
Sai dai kuma ya ce duk da ana samu kalubale wajen sake maida masu gudun hijira matsugunan su, duk haka dai ana samun nasara bakin gwargwado.
Johnson ya gode tare da jinjina wa Buhari, wanda ya kira shugaba na yankin Kasashen Sahel, na Afrika ta Yamma baki daya.
Sannan kuma ya yaba masa yadda ya ke jan sauran kasashen wajen kara dankon zumunci ta fannoni da dama da kasar Ingila.