Buhari ya bayyana wa Shugaban Ghana dalilan rufe kan iyakokin Najeriya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa Shugaban Ghana cewa ba wai saboda kayan abinci kadai ba ne, musamman shinkafa da ake ta yamadidi a kan ta da ake sumogal cikin Najeriya ba.

Buhari ya shaida wa Nana Akufo-Addo na Ghana cewa sun san ana shigo da tulin manyan makamai da miyoyin albarusai da muggan kwayoyi ta kan iyakokin Najeriya, wadanda ake shigo da su ta hanyar biyowa daga makwautan kasashe.

“Idan aka tare motocin daukar shinkafa da ake sumogal cikin kasar nan, da an bincika sai ka ga an samu muggan kwagoyi a ciki, da muggan makamai a karkashin kayan abinci. Wannan abu ya yi muni kuma ya haifar da mummunar illa ga kasar nan. Kuma ko ma wace kasa ce ta fuskanci haka, to abin zai zamar ma ta babbar matsala.” Haka Buhari ya shaida masa.

Sai dai kuma Buhari ya ce ko kadan ba ya jin dadin yadda rufe kan iyakokin Najeriya ya haifar da kuncin rayuwa a kasashen da ke makwautaka da Najeriya.

“Ba mu jin dadin yadda wannan rufe kan iyakoki ya haifar da kunci a makwautan kasashen mu. To amma fa ba za mu bar kan iyakokin mu a bude ba, ana amfani da su ana shigo mana da ababen da ke lalata mana rayuwar matasa ba.”

Kasashen da ke makautaka da Najeriya sun hada da Jamhuriyar Nijar, Kamaru, Chadi, Benin.

Buhari ya ce dukkan kasashen Yakin Sahel su na fama da fantsamar muggan makamai a kasashen.

Ya ce dukkan su matsalar duk kusan daya ce tun daga Mali, Chadi, Burkina Faso, Nijar da Najeriya.

“Amma dai mu a Najeriya mun fi sauran kasashen fama da wannan babban bala’i.” Haka Buhari ya furta.

Dangane da lokacin bude kan iyakokin kuwa, Buhari ya shaida masa cewa ba za a bude ba tukunna, har sai kwamitin da gwamnati ta kafa a kan iyakokin ya kammala binciken sa, ya mika wa gwamnati, an duba, kuma an ga cewa idan an bude, to babu wata illa.

Sai dai kuma duk da shugaban na Ghana ya fahinci bayanin da Buhari ya yi masa dangane da yanayin da Najeriya ta samu kan ta, har aka rufe kan iyakokin, duk da haka ya ce ya na rokon Najeriya ta sake duba lamarin, domin Ghana na ta dogaro sosai da cinikayyar da kasar ke yi da Najeriya.

Share.

game da Author