Boko Haram sun yi garkuwa da matafiya bakwai a titin Damaturu zuwa Maiduguri

0

Wani matafiyi da ya tsira daga harin Boko Haram a titin Damaturu zuwa Maiduguri ya bayyana cewa Boko Haram sun yi garkuwa da matafiya bakwai a wannan hanya.

Kamar yadda wannan matafiya da baya so a fadi sunan sa ya bayyana, ya ce Boko Haram sun tare hanyar sanye da kayan sojoji sannan dauke da manyan bindigogi.

” Wani motar fasinja, kirar Golf ne ta fara fadawa shingen Boko haram din inda suka umarci kowa ya fito daga cikin motar. Ana haka ne fa sai wata motar fasinja mallakin gwamnatin jihar Adamawa wato Adamawa sunshine express ta fada ciki ita ma.

” Boko Haram din sun umarci wasu mutane biyu daga cikin wannan mota su fito su bisu cikin motar su tare da wadanda suka tattara daga motar Golf.

” Yadda Allah ya sa muka tsira shine bayan mun hango afkawar wadannan motoci sai muka ci burki sannan direbar motar mu ya juya kan motar yayi baya da gudun tsiya. Haka muka yi har muka koma garin Jakana.

” A can garin mun cimma tarin motoci da suka dakata domin su hango wulkawar wani mota daga can ya wuto kafin ci gaba tafiyar su.

Matafiyin ya ce daga baya dai bayan sun hango wani mota ya biyo hanyar dukkan su sai suka yi shahada suka afka kan titin kawai suka ci gaba da tafiya.

Idan ba a manta ba jami’an sojoji sun yi kokarin kwashe mazauna wasu kauyuka dake kusa da inda aka yi garkuwa da fasinjojin gwamnan jiha Babagana Zulum ya hana wannan abu.

Share.

game da Author