BOKO HARAM: Sojojin-taron-dangi sun ‘kashe kwamandan ISWAP’

0

Sojojin taron dangi na kasa-da-kasa (MNJTF), sun bayyana kashe wani babba a cikin manyan kwamandojin kungiyar ta’addanci ta ISWAP.

MNJTF ta bayyana cewa sun kashe mai suna Khalifa Umar, a wani harin jirgin sama da aka kai mabuyar su Umar, a yankin Tabkin Chadi, cikin wani kauye mai suna Tunbus Sabo.

Sanarwar da kakakin MNJTF Timothy Anthigha ya sa wa sannan ya fitar, ta bayyana cewa an kashe Khalifa “yayin wani farmaki da aka kai wa kungiyar ta su ISWAP a yankin Chadi.”

Kanar Anthigha ya kara da cewa an kashe Umar, wanda shi ne babban kwamandan Boko Haram, bangaren ISWAP na uku a jerin shugabanni ko kwamandojin su.

“An kashe shi a harinn da aka kai musu ta jirgin yaki jiya a Tunbum Sabo.”

“Har ila yau, Anthigha ya kara da cewa “Umar na da muhimmanci a kungiyar, kasancewa kuma shi ne babban alkali na kungiyar.”

An kuma “kai wani farmakin ta jirgin yaki inda aka sake samun nasarar kashe qwasu kwmandojin yaki na ISWAP, su uku.”

Daga nan sai Anthigha ya shaida cewa nan gaba zai kara fitar da bayanin dalla-dalla dangane da yadda gumurzun yaki ya wakana da kuma.

Cikinn makon jiya ne MNJTF suka bayyana cewa sun kai farmaki a sasanin ISWAP a Tumbun Madayi, inda suka kashe ‘yan ta’adda masu yawa.

“An yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da kwaman dojin su da dama, a inda suke taruwa su na atisaye da horar da mayakan su.”

Sai dai kuma har yanzu MNJTF ba su bayyana hotunan gawarwakin kwamandojin da suka ce sun kashe ba.

Amma dai idan har hakan ya tabbata, to wannan kisan babbar nasara ce.

Share.

game da Author