BOKO HARAM: Najeriya ta siyo jiragen sama masu aman wuta

0

Babban Hafsan sojojin saman Najeriya Sadique Abubakar ya bayyana cewa Najeriya ta siyo sabbin jiragen yakin sama masu aman wuta.

Sadique ya ce wadannan jirage na daga cikin jirage da makaman da gwamnati ta siya.

Ba wadannan ba ya ce akwai da dama da za su iso Najeriya a watan Faburairu.

” Na tabbata kuna sane da irin makaman da rundunar ‘yan sanda suka shigo da su su ma, sannan kuma ina fatan baku manta da amincewa da jami’an tsaron sa kai da Buhari yayi ba?

” Gwamnati ta yi wannan karfin hali ne domin kakkabe sauran burbudin Boko Haram da kuma kawo karshen hare-hare da garkuwa da mutane da ‘yan bindiga suke yi musamman a yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.

” Sannan kuma muna tattaunawa da kasashen dake zagaye da tafkin Chadi domin daidaituwa a matsaya daya kan yadda za a gama da Boko Haram.

” Babban abinda muke roko wurin mutane shine su rika taimakawa jami’an tsaro wajen samun nasara a wannan aiki da suka saka a gaba.

” Lallai jami’an tsaro na bukatar irin wannan hadin kai domin a samu nasarar kawo karshen matsalolin tsaro da ya addabi muranen kasar nan da yanzu haka ana samun nasara matuka.

Sadique ya kara da cewa wadannan jirage za su ba sojojin karfin guiwar tunkarar Boko Haram a inda suke boye a can cikin kungurmin daji da ke ba da wahala a da.

Sannan kuma ya ce suma mahara baza su sha da dadi ba domin za a rika afka musu ne ta ko-ina ana musu ruwar balbalin wuta daga sama.

Share.

game da Author