BOKO HARAM: Gumurzun yaki a Jakana da Sambisa

0

Jiya Asabar da dare Boko Haram sun kai hari a kauyen Jakana, wanda ke kilomita 42 kafin shiga Mauduguri, babban birnin Jihar Barno.

Garin Jakana ya na kan hanyar Maiduguri zuwa Kano, kuma ta wannan hanya ce kadai ake iya shiga da fita Maiduguri daga sauran jihohin kasar nan baki daya.

Kutsawar su cikin garin ke da wuya sai suka rika bude wuta, su na harbe-harbe. Sai dai kuma sojojin Najeriya da ke girke kusa da Jakana sun kai dauki, inda take yaki ya barke har aka karkashe ‘yan Boko Haram da yawa.

Wani Babban Kwamandan C-JTF, Bello Dambatta, ya shaida wa wakilin mu cewa Boko Haram sun kutsa cikin Jakana wajen 7:30 na dare. Sai dai kuma an kashe da yawan su a lokacin da sojoji suka yi musu rubdugu.

Ya kara da cewa bai zai iya cewa ga yawan Boko Haram da aka kashe ko aka raunata ba, amma dai ya ga gawarwaki takwas da aka kwaso.

Idan na manta ba, cikin 2019 sai da sosoji suka kwashe mutanen kauyen Jakana baki dayan su, aka maida su sansanin masu gudun hijira.

Sojoji sun yi haka ne bisa dalilin aikin da suka yi na fafarar Boko Haram da ke yankunan kewayen kauyen.

Sun kuma yi zargin cewa wasu ‘yan Boko Haram na shigowa cikin kauyen su yi basaje, amma mazauna kauyen ba su tona musu asiri.

A wancan lokacin dai sojoji sun datse hanyar shiga Maiduguri daga Kano da Damaturu, har matafiya suka yi kwanan kan hanya.

Wuta A Dajin Sambisa

Rundunar Sojojin Sama da ke Yakin Boko Haram a karkashin Operation Lafiya Dole, sun bada sanarwar kai wa Boko Haram wani mummunan hari cikin Dajin Sambisa.

Sanarwar da Kakakin OLD, Abikunle Daramola ya fitar jiya Asabar a Abuja, ta bayyana cewa an kai wa Boko Haram wannan gagarimin hari ne ta jirgin yaki, inda aka ratattaka musu wuta, aka kashe masu yawa.

“An hango su ne ta na’ura su na gangami su na taruwa a karkaahin wata bishiya, inda suke shirin kai hari a wani sansanin sojoji.

“Sannan kuma an lura suna tuka wata motar yaki bayan wasu bishiyoyi. To daga nan aka hanzarta tashin jirgin yaki, wanda aka garzaya aka ruka yi musu ruwan wuta ta sama.

“An yi ta ragargazar su, sannan wadanda suka yi kokarin gudu ta hanyar tserewa ta gangaren Bula Bello, su ma sun sha wuta.” inji Daramola.

An dai kiyasta cewa daga 2009 farkon fara rikin Boko Haram zuwa 2019, an kashe mutane kumanin 40,000.

Share.

game da Author