Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kananan Hukumomin Pankshin, Kanke da Kanem, ya yi tir da kisan da Boko Haram suka yi wa Daciya Dalep, wani dalibi na Jami’ar Maiduguri.
Honorabul Gagdi, ya yi wannan kakkausan tir ne kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito a Jos, yau Laraba, inda ya ce wannan kisan dabbanci ne.
NAN ta ruwito cewa Boko Haram sun sace Dalep makonni biyu da suka gabata, a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta komawa Jami’ar Maiduguri daga Jos.
A ranar Talata ce Boko Haram suka saki bidiyon da suka nuno yadda suka kashe dalibin.
“Na yi Allah-wadai da babbar murya dangane da wannan kisan gilla da Boko Haram suka yi wa Daciya Dalep, dan kabilar Jing, cikin Karamar Hukumar Pankshin, wanda ya ke karatu a Jami’ar Maiduguri.
“Hankali na ya dugunzuma dangane da irin mummunan kisan gillar da aka yi wa wannan matashi, wanda ni ba ma zan yi fatan a yi wa abokin gaba na irin wannan mummunan kisa ba.
“Wannan kisa ya kara nuna irin mawuyacin halin da al’ummar Arewa maso Gabas na kasar nan ke ciki.”
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatoci tun daga sama har kasa su tashi tsaye domin kawo karshen wannan mummunan bala’i na Boko Haram.
Ya yi kiran ‘yan Najeriya su kara bai wa jami’an tsaro goyon baya domin kai ga nasar ar wannan kalubale wanda ke neman kawo barazana ga dorewar zamantakewar kasar nan.
Idan ba a manta ba, farkon wannan mako ne Boko Haram suka kashe wani babban fasto a jihar Adamawa, bayan kin karbar tayin naira milyan 50 da aka yi musu.