BOKO HARAM: Chadi ta janye sosojin ta 1,200 daga Najeriya

0

Kasar Chadi ta janye sojojin ta daga yarjejeniyar gangamin yaki da Boko Haram da aka kulla da ita a Najeriya.

Wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa, AFP ya wallafa jiya Asabar, ya ruwaito kakakin dakarun Chadi, Kanar Azem Bermudoa na cewa sojojin Chadi sun koma gida, daga aikin da aka tura su yi a Najeriya.

“A yanzu dai babu sauran sojojin mu ko daya a Najeriya, duk sun dawo cikin kasa. Za mu karkasa su can a Yankin Tafkin Chadi kusa da kan iyaka, domin ci gaba da gudanar da tsaro a yankunan kan iyakoki.”

Kimanin sojojin Chadi 1,200 aka turo Najeriya domin taya kasar yaki da Boko Haram, a wata yarjejeniya da kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi suka kulla a cikin watan Yuli, 2019.

Wadannan kasashe uku na fama da ta’addancin Boko Haram, kuma duk sun hada kan iyaka da Najeriya.

Ba a dai san dalilin janyewar ba, amma kuma Babban Kwamandan Sojojin Kasar Chadi, Tahir Erda Tahiro ya ce sojojin kasar sa sun kammala aikin da aka tura su yi a Najeriya. Don haka idan har za su koma, to said an sake kulla wata yarjeniya sabuwa kenan.

Tun bayan kulla wannan yarjejeniya an dan samu karancin kai yawan hare-hare a sansanonin sojoji da Boko Haram ke kai wa farmaki.

Sai dai kuma ba a san tasirin da janyewar sojojin Chadi zai iya haifarwa ba a yankin Arewa maso Gabas, inda a yanzu kuma Boko Haram sun dawo da kai hare-hare gadan-gadan.

An kasa jin ta bakin kakakin yada labarai na sojojin Najeriya, a lokacin da ake tattara wadannan bayanai.

Share.

game da Author