Binta Spikin, Kakakin Yada Labarai ta tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ta koma APC.
Binta ta bayyana ficewar ta daga PDP ta koma APC a ranar Laraba.
Ta fita daga PDP kwana daya bayan shugaban jam’iyyar PDP na riko na jihar Kano, Rabiu Sulaiman ya fita daga PDP ya koma APC.
An bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ubangidan ta a siyasa, Rabiu Sulaiman ne ya ja ta zuwa APC, ta raba hanya da Kwankwaso.
PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda Bichi ya koma APC daga PDP, kwanaki kadan bayan da Kotun Koli ta kara jaddada nasarar Gwamna Abdullahi Ganduje na APC a jihar Kano.
Sipikin wadda a Kano ta yi kaurin suna cikin kungiyar rajin matsin-lamba, wato NGO, ta bayyana cewa tun bayan zaben 2019 ta raba hanya da Kwankwaso, amma sai a wannan lokacin ne ta fito fili ta bayyana. Wato daga cikin ‘yan PDP da suka koma APC sun hada da Aisha Kaita, Muhammad Tarauni, Idris Bala da aka fi sani da Dan Kwankwasiyya.
Kakakin Jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Shehu Sagagi bai amsa kiraye-kirayen da wakilinmu ya yi masa ba, domin jin ta bakin sa.
Yayin da wasu ‘yan PDP suka koma APC a Kano, a yanzu dai ta kara fitowa fili cewa kusan duk ‘yan PDP ne a cikin jam’iyyar APC a Kano, jihar da ta fi sauran jihohin kasar nan tasiri a siyasa.
Shi kan sa Shugaba Muhammadu Buhari, bayan ya taya Ganduje murnar yin nasara a Kotun Koli, ya bayyana cewa da APC ba ta yi nasara a Kotun Koli ba, to da sun shiga tsilla-tsilla a Kano.