BIDIYO: Kwankwaso shirgegen ‘mayaudari ne’ – Inji Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso mayaudari ne sannan kan sa kawai ya sani.

Ganduje ya kara da cewa tsautsayi ne ya hada su da Kwankwaso domin kuwa sun yi fama da shi a lokacin da suke tare.

” Abu daya da ya taba tada min da hankali har ya hana ni barci shine yadda aka kai Kwankwaso wurin Buhari gab da zabe ba tare da na sani ba.

” Mutum mara gaskiya kamar Kwankwaso ace wai an saka da shi zuwa waurin mutum mai gaskiya kamar Buhari, ba tare da na sani ba yayi min ciwo matuka a gab da zaben 2019.

” Sannan kuma bayan sun gana da Buhari, sai kawai aka ji kuma shugaban majalisar dattawa a wancan lokaci, ya fice daga APC din.

Share.

game da Author