Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya bayyana cewa ya na da yakinin zai yi nasara a shari’ar da yanzu haka ake kan yi a Kotun Koli.
Tsohon Gwamnan Bauchi Mohammed Abubakar na APC ne ya shigar da karar rashin amincewa Da kayen da ya sha a hannun Bala na PDP a zaben 2019.
Yayin da ake jiran sakamakon hukuncin kotu, Gwamna Bala wanda yanzu ke jiyya a wani asibiti a Landan, sakamakon wata rashin lafiyar da ba a bayyana ta ba, ya ce ya na da yakinin zai yi nasara.
Daga nan kuma ya ce da yardar Allah ya kusa dawowa gida domin ya fatattaki wasu da ya kira, “’yan cikin gwamnatin sa masu son a yi nasara a kan sa.”
Ya kara nuna cewa nasara a bangaren sa ta ke, kamar yadda kakakin sa Mukhtari Gidado ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a yau Talata.
“Gwamna ya kusa dawowa, kuma zai dauki kwakkwaran mataki a kan masu neman ganin ya yi rashin nasara da masu yi masa zaon-kasa a cikin gwamnatin sa.
“ Gwamna ya ce akwai da yawa masu neman ganin bayan sa da a yanzu haka suka bayyana, su na kokarin Kotun Koli ta soke zaben sa. Amma dai ya bayyana cewa ya na da kwarin guiwa cewa shi ne zai yi nasara a kotun.
“Yanzu haka ina jiyya a asibiti a Landan, amma mu na da yakini da kuma imani ga Allah cewa nasara a gare mu ta ke. Ina taya mu murna, kuma ina jinjina muku.
Daga nan ya yi alwashin ci gaba da jagoranci mai adalci, gaskiya, daidaito da mutunta al’umma a jihar Bauchi.
Kuma ya ce zai saka wa dukkan wadanda suka taimaka masa wajen tabbatar da samun nasarar da ya yi a zaben 2019.