Barcelona ta kori mai horas da ‘yan wasan ta

0

Kungiyar Barcelona FC ta Spain ta kori kociya Ernesto Valverde, bayan shafe shekaru biyu da rabi kacal a kulob din.

An maye gurbin sa da tsohon kociyan Real Betis, Quique Setien mai shekaru 61. Setien zai rike Barcelona tsawon shekaru biyu da rabi, wato zuwa tsakiyar 2022.

Duk da Ernesto ya ci kofin La Liga har sau biyu a jere, mahukunta da shugabannin Barcelona ba su gamsu da irin salon sa ba, musamman ganin yadda Roma ta fitar Barcelona a Gasar Champions League a kakar 2017/2018.

Sannan kuma shugabannin Barcelona sun nuna fushin yadda Liverpool ta kori Barcelona a Gasar Champions League ta 2018/2019.

Duk da cewa Barcelona ce ta daya a teburin La Liga, inda ta ke kankankan da Real Madrid wajen yawan maki, shugabannin Barcelona sun ji haushin yadda kungiyar Valencia ta lashe kofin Supercopa a hannun Barcelona a wasan karshe na 2019.

Sannan kuma haushin ya karu cikin makon da ya gabata, ganin yadda Atletico Madrid ta kori Barcelona a wasan kusa da na karshe, na Supercopa, a Riyadh, babban birnin Saudi Arebiya.

Magoya bayan Barcelona sun yi zaton za a maye Valverde ne da tsohon Dan wasan kungiyar, Xabi Harnendez.

Sai dai kuma za a iya sa ran daukar Xabi din nan gaba, ganin cewa shi ma sabon kociyan na yanzu shekaru biyu da rabi kadai aka kulla yarjejeniyar zai yi a Barcelona.

Share.

game da Author