Ban taba ganin mutum mai son kan sa ba kamar Kwankwaso – Ganduje

0

A daidai lokacin da jama’a da dama ke maganganun cewa wasu da suka ci albarkacin siyasar tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso na ci gaba da yi masa sakayyar cin amana, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana dalilin da y ace ya sa shi raba hanya da Kwankwaso.

Ganduje wanda ya yi wa Kwankwaso mataimakin gwamna tsawon shekaru takwas, kuma aka tsaida shi takarar gwamna a 2015, har ya yi nasara, ya bayyana cewa, “idan dan Adam ya so kan sa, wannan ba wani abu ba ne, domin son kai na a jikin kowa. To amma ni dai ban taba ganin mutum mai son kan sa ba kamar Kwankwaso.”

Haka Ganduje ya bayyana a ranar Alhamis din nan, a lokacin da ya karbi shugaban jam’iyyar PDP na Kano, Salisu Bichi da wasu da suka canja sheka daga PDP suka koma APC a jihar.

Sun yi canjin shekar ne kwanaki kadan bayan Kotun Koli ta kara jaddada nasarar zaben da Ganduje ya samu.

“ Dukkan mu da ke nan a zaune, a baya da can a karkashin Kwankwaso mu ke. Kuma mu ne muka cicciba shi ya kai matakin da ya kai. Amma babu kamai a cikin sa sai tsananin son ran sa kawai.” Inji Ganduje.

Ganduje ya ce da shi aka kafa Tafiyar Kwankwasiyya, domin ya na tare da Kwankwaso tun kafin 1999 lokacin da ya yi masa takarar Mataimakin gwamna.

A na sa bayanin, Sulaiman Bichi ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano su mara wa Ganduje baya.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda Kakakin Yada Labarai ta Kwankwaso, mai suna Binta Spikin ita ma ta bi ubangidan ta a siyasa, Sulaiman Bichi suka koma APC a Kano.

Share.

game da Author