Bakauye da magoya bayan sa 30,000 sun fice daga PDP zuwa APC a jihar Zamfara

0

Dan takarar gwamnan jiha Zamfara a jam’iyyar PDP a zaben 2019 kuma tsohon dan majalisar tarayya Ibrahim-Shehu Bakauye da magoya bayan sa 30,000 sun fice daga PDP zuwa APC a jihar Zamfara.

Wannan ficewa da suka yi koma baya ne matuka ga jam’iyyar PDP a jihar Zamfara da PDP ke mulki.

Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Zamfara na bangaren da basu ga maciji da na bangaren gwamnan Jihar, Nasir Milo ya bayyana cewa shugaban su Shehu Bakauye ya canja sheka kuma dukkan su suna tare da shi a wannan matsayi da aya dauka.

Milo ya ce bayan ganawa da suka yi da tsohon gwamnan jihar AbdulAziz Yari, gaba dayan su sun yi bi kuma sun koma APC karkakakaf dinsu.

Ya ce magoya bayan su akalla 30,000 ne daga kananan hukumomi 14 suka amsa kira duk suka fice daga PDP zuwa APC.

” Hakan da muka yi nune ne cewa jam’iyyar APC ce jam’iyyar da ta fi karfi a jihar Zamfara.

Share.

game da Author