Ba makusanta na ke ‘juyani ko tafiyar da gwamnati na ba’ – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya musanta zargi da maganganun da ake yawan yayatawa cewa wasu tsirarun makusantan sa da ake kira ‘cabals’ ne ke yin yadda suka ga dama wajen tafiyar da gwamnatin sa.

“Ni da kai na ne na kewaya fadin kasar nan ya yi kamfen, kuma ni din dai aka zaba a matsayin shugaban kasa har sau biyu. Ni ne na yi rantsuwar karbar mulki kuma ni kadai ne ke da karfin ikon zartaswa a matsayin Shugaban Kasa.”

Haka Buhari ya bayyana wa Mujallar Interview wadda ta yi tattaunawa ta musamman da shi ta hanyar tura masa tambayoyi ta e-mel.

’Yan Najeriya da dama, ciki har kuwa da uwargidan sa Aisha Buhari, sun yi ikirarin cewa akwai wasu tsirarun makusantan Buhari da ta kira ’yan-ba-ni-na-iya da ke da tasirin sa baki wajen sha’anin gudanar da al’amurran mulkin Buhari.

Aisha ba sau daya ta sha zargin cewa wasu na yin yadda suka ga dama wajen tafiyar da gwamnatin Buhari, alhali milyoyin ‘yan Najeriya da suka zabe shi na cikin damuwar yadda lamarin ke tafiya.

Wasu daga cikin wadanda ake nunawa da yatsa ana cewa su ne ‘cabal’, sun hada da Mamman Daura, wanda dan uwan sa ne, sai wani makusancin sa, Sama’ila Isa Funtua da kuma Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, wato Abba Kyari.

Kwanakin baya ma Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce akwai ‘cabals’, amma su ba mayunwata ba ne, mutane ne masu mutunci da suka cancanta a rika ganin mutuncin su a fadin kasar nan.

Shi kuwa jagoran PDP, Bola Tinubu, ya ce maganar wasu ‘cabals’ duk tatsuniya ce kawai da mutane suka kirkiro.

An tambayi Buhari dalilin da ya sa ba a jin Kwamitin Tattalin Arzkin Kasa na Doyin Salami ba ya wani tasiri, kuma ba a jin aikin sa.

Sai Buhari ya bayyana cewa kwamitin ya na aikin sa, kuma ba lallai ne sai idan an rika jin kwamitin a kakafen yada labarai ne kadai za a iya sanin ya na aiki ba.

Buhari ya kara jaddada aniyar sa ta ceto ‘yan Najeriya milyan 100 ta hanyar sama musu ayyukan yi, duk kuwa da yawan al’ummar da ke kara yawa a kasar nan.
Sannan kuma ya kara yin alkawarin mika mulki ga wanda ya yi nasara a zaben 2023.

Batun dangantaka da mataimakin sa Osinbajo kuwa, Buhari cewa ya yi, “dangantaka na nan daram. Ko kuwa ya yi maka wani korafi ne?”

Share.

game da Author