Hukumar kula da jiragen Kasa ta kasa ta karyata rade-radin da ake ta yadawa wai an kai wa jirgin kasa da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja hari a garin Katari.
Shugaban Hukumar NRC Fidet Okhiria ya karyata wasu kafafen yada labarai da suka yada cewa mahara ne suka afkawa jirgin kasan a Katari.
” Wannan batu babu gaskiya a ciki. Wasu yara ne suka jefi jirgin da dutse har ya fasa gilashin jirgin. Jami’an tsaro da ke aiki a jirgin sun tabbatar mana cewa babu wani mai kama da haka da ya auku a garin Katari yau Alhamis.
” Ina kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalin su cewa an samar da matakan tsaro a cikin jirgin da wajen jirgin domin tsaron matafiya.