Attajirai 22 sun fi gaba dayan matan Afrika milyan 325 kudi

0

Hamshakan Attajiran duniya su 22, wato daga na 1 zuwa na 22 a jerin su, duk sun fi ilahirin matan da ke Nahiyar Afkira kakaf kudi. Wani sahihin rahoto ne ya tabbatar da haka.

Rahoton wanda Oxfam ta buga a ranar Litinin, ya nuna cewa matan da ke fama da kuncin talauci a duniya sun kai kashi sama 3 bisa 4 na wadanda ba su da aikin da ake biyan su albashi, lada ko alawus.

Kamar yadda Oxfam ta bayyana, a cikin rahoton ta kafin Taron Duniya na Arzikin Tattalin Kasashe a Davon, kasar Switzerland wannan makon, ta ce, “Hamshakan attajirai 22 na duniya sun fi mata milyan 325 na Afrika dukiya da kudi.”

Oxfam ta ja hankalin cewa tattalin arziki ba ya yin tasirin samun ci gaba a cikin mata, musamman a Afrika, domin yawancin su aikin da suke yi ya fi karfin ladar da ake biyan su. Wasun su da dama kuwa ko aikin ma ba su da shi.”

Shugaban Oxfam, Danny Sriskandarajah, ya ce: “ Yayin da aka ce namiji 22 masu arziki a duniya su na da kudin da ya haura dukiyar gaba dayan matan Afrika milyan 325, to wannan ya na nuna kenan tattalin arziki ya fi samar wa maza sukuni, babu ruwan sa da mata kwata-kwata.”

“Idan har da kaske shugabannin duniya ke yi cewa sun a son talauci da ratar da ke tsakanin maza da mata, to ya zama wajibi su kara samar da tsare-tsaren da mata za su samu shiga wajen dukkan hanyoyi da dabarun samu ci gaba a rayuwa, kamar yadda a yanzu maza ke samu.

Cikin wannan makon ne za a yi taron hamsahkan kasashen duniya a kan tattalin arzikin kasashe a Davon, cikin kasar Switzerland.

Wannan rahoto dai bai bayyana suayen attajiran 22 ba. Sai dai kuma mafi hamshaka a arziki a Afrika, kuma wanda ya fi dukkan bakaken fata kudi a duniya, wato Aliko Dangote, daga Afrika ya ke, dan asalin Kano, Najeriya.

Share.

game da Author