Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta gudanar kan adadin yawan mutanen dake busa taba sigari a duniya ya nuna cewa an samu ragowa a yawan mutanen dake busa taba.
WHO ta ce an samu nasara a haka ne a dalilin hada hannu da gwamnatocin kasashen duniya da kungiyar ta yi wajen fadakar da mutane game da illar busa taba sigari.
Da yake tofa albarkacin bakin sa kan wannan batu shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya ce samun wannan sakamakon nuni ne cewa za a samu nasarar da ya fi haka idan har gwamnati ta yi dakan maza wajen ganin ta kafa dokokin hana mutane busa taba a duniya.
Idan ba a manta ba bincike ya nuna cewa busar taba na ajalin mutane miliyan Takwas a duniya duk shekara inda a cikin wannan yawa akwai mutane miliyan 1.2 wanda ke rasa rayukan su a dalilin shakar hayakin taba.
Likitoci sun ce ana fama da cututtuka kamar su hawan jini, cutar koda, cutar daji, ciwon siga da sauran su a dalilin busa taba.
Sakamakon wannan bincike da kungiyar ta gudanar ya nuna cewa mutane biliyan 1.397 ne ke busa taba sigari a duniya a shekarar 2000 amma hakan ya ragu zuwa biliyan 1.3337 a shekaran 2018.
A bangaren mata masu busa taba a duniya ya ragu daga miliyan 346 a shekaran 2000 zuwa miliyan 244 a 2018.
A bangaren maza kuma sakamakon binciken ya nuna cewa za a samu ragowar maza miliyan daya da za su daina busa taba a shekarar 2020.
Binciken ya kuma nuna cewa yara miliyan 43 masu shekaru 13 zuwa 15 na busa taba sigari a duniya.
WHO ta yi hasashen cewa nan da shekaran 2025 mata miliyan 32 daga cikin miliyan 244 din dake busa taba ne za su daina kwata-kwata. Sannan maza miliyan biyar za su daina busa taba a duniya a shekarat 2025.
Discussion about this post