An bindige babban dan siyasa a ruguntsimin murnar lashe zabe

0

An bindige dan takarar sanata a zaben 2019 da ya gabata, mai suna Ndubuisi Emenike.

Ana zargin cewa wani jami’in tsaro na ‘Civil Defence’ (NSCDC) da ke tsaron sa ne ya dirka masa bindiga.

Mamacin dai ya fito takarar sanata ne na Imo ta Arewa a zaben 2019.

PREMIUM TIMES ta gano cewa jami’in tsaron wanda ya dirka masa bindiga, ya bi shi ne sun tafi tare wurin wata walimar murnar lashe zabe.

An bindige Ndubuisi ranar Lahadi wajen karfe 5 na yamma, a garin da aka haifi Miriam Onuoha, a Umanachi, Isiala, da ke cikin Karamar Hukumar Mbano da ta jihar Imo.

A wajen ruguntsimin taya Miriam murna ne tsautsayi da karar-kwana su ka ratsa, aka bindige babban dan siyasar.

Onuoha ce ’yar takarar APC, kuma ita ce ta lashe zaben da aka yi na ‘inconclusive’, ranar Asabar din da ta gabata.

An ce an dankara wa Emenike harbi ne a lokacn da ake tsakiyar ruguntsimin bikin murna, kwana daya bayan Onuoha ta lashe zaben, kuma INEC ta tabbatar da ita.

Wani da mummunan al’amarin ya faru a gaban sa, ya ce jami’in tsaron ya rika harbi a sama ne babu kakkautawa, kafin daga baya ya kuskure, ya dirka wa maigidan na sa bindiga.

Bayan an kwashi Emenife an garzaya da shi asibiti, ba a dade ba, sai likitoci suka bayyana cewa ya mutu.

Kakakin ’Yan sandan Imo, Orlando Okeokwu ya tabbatar da faruwar lamarin. Sannan kuma ya ce tuni an damke jami’in na NSCDC, domin a bincike shi.

Share.

game da Author