‘Akwai baragurbin mutane’ kewaye da Buhari -Obla, Tsohon Hadimin Shugaban Kasa

0

Tsohon Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Mai Kwato Dukiyar Sata, Okoi Obono-Obla, ya bayyana cewa tsarin shari’a ya lalace a Najeriya, ya koma rufa-ido kawai.

Da ya ke tattaunawa da wata jaridar online mai suna Calitown.com, wadda ake watsawa a Cross River, Obla ya ce a yanzu babu irin daren da jemage bai gani ba. Don haka, “Ni a yanzu na yqnke kauna da duk wani imani da na ke da shi a kan Najeriya.”

“Na shafe shekara da shekaru ina gaganiyar rajin kare al’umma, ina kokarin ganin komai ya tafi daidai. Amma a yanzu na gane ba son gyara ake yi ba. Gaskiya guyawu na sun yi sanyi da tsarin shari’a a Najeriya.

” Akwai gungun wasu mabarnata a cikin gwamnati da ba za su taba bari abubuwa su tafi daidai ba.

“Akwai kuwa wasu baragurbin mutane da ke kewaye da Shugaban Kasa.” Wadannan mutane inji Obla, ba za su taba bari a yi abin kirki ba.

Idan ba a manta ba, Buhari ya cire Obla cikin watan Sarumba, bayan an zarge shi da harkalla, a matsayin sa ba Shugaban Kwamitin Kwato Kayan Sata na Kayan Gwamnati.

Sai dai a na sa bangaren, ya ce bai ci sisin kwabon kowa ba, kawai dai wasu gungun mutane ne ke neman raba shi daga cikin gwamnati, don su ci gaba da ‘cin karen su babu babbaka’.

“Shugaban Hukumar ICPC ne ya rika kitsa min tuggu, saboda kawai ya na ganin kamar ni za a ba shugabannin ICPC. Domin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo suna na ya bayar.”

PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin Yada Labarai ta ICPC, Rashidat Okoduwa, wadda ta ce babu wani takun-saka tsakanin Shugaban ICPC da Obla.

“Abin da kawai mu ka sani ne cewa an zarge shi da harkalla, mu kuma muka gayyqce shi domin ya zo ya kare kan sa. Wannan shi ne kawai abin da ke tsakani. Don haka zuwan sa ya kare kan sa ya fi da ya rika zuwa ya na wasu surutai a gefe.”

Yadda Na Fallasa Watandar Bilyoyin Daloli

A cikin tattaunawar, Obla ya ce ya fallasa yadda aka rika wawurar bilyoyin daloli a kasar nan. Daga ciki, ya bayar da labarin wasu da ya ce ya yi mamakin yadda aka binne watandar, bayan ya fallasa ta.

“Zamanin mulkin Obasanjo, CBN a karkashin shugabancin Charles Soludo ya bai wa bankuna dala bilyan 7 domin ceto su daga durkushewa. Na binciko wannan batu, na rubutawa wa CBN wasika, amma sai aka maido min amsa cewa wai gwamnati ce ta sa aka rufe wannan magana.”

Wani misali kuma da Obla ya sake bayarwa shi ne yadda aka yi kashe-mu-raba da kudaden cinikin rijiyar mai da aka sayar wa kamfanin Mobil. Obla ya ce kamata ya yi a saida rijiyar dala bilyan 2.5, amma sai aka sayar da ita dala bilyan 650 kacal

Share.

game da Author