Rundunar Tsaro ta NSCDC, ta Jihar Adamawa ta bayyana cewa ta kama wasu rikakkun masu garkuwa da mutane, wadanda suka addabin garin Mubi da kauyukan da ke kewaye.
Da ya ke gabatar da masu garkuwar a gaban manema labarai, Babban Kwamandan NSCDC na jihar, Nurudddeen Abdullahi ya ce an kama su ne a ranar Juma’a da ta gabata bayan an samu hadin kai da taimakon jami’an sojoji da mafarauta na Mubi.
Ya ce an kamo su ne bayan da wasu masu kishin jama’a da kasar nan sun tsegunta wa jami’ai mabuyar masu garkuwar.
“Dukkan wadanda muka kama din sun tabbatar da cewa su ne suka rika yin hare-haren garkuwa da mutane a yankunan Kananan Hukumomin Maiha da Mubi da kewayen su.
“Yanzu dai wadanda ake zargin su na hannun sashen binciken manyan laifuka na CID domin ci gaba da yi musu tambayoyi, daga nan kuma a gurfanar da su kotu.” Haka Abdullahi ya bayyana.
‘Kowa Ya Zama Mai Garkuwa da Mutane’
Yawan hare-hare da garkuwa da mutane da ake yi a yankunan babu kakkautawa, ya sa jama’a da dama sun daina kwana gidajen su, gudun kada aka yi musu tattaki hara gida a yi awon-gaba da mutum.
Da ya ke magana a kan wannan babbar matsala, tsohon kakakin majalisar jihar Adamawa, Sadik Ibarahim Dasin, ya ce, “a wani irin yanayi mai daure kai mai kama da za a iya cewa wasu daga kasashen waje sun mamaye Karamar Hukumar Fufore, masu garkuwa sun yi kaka-gida a yankin na Fufure.
“Kai yanzu fa abin ya kai har ma jama’a sun rigaya sun saba da garkuwa da mutane, ya zama jiki. Saboda ba su iya yin komai a kai. Ba gwamnati ce kadai ta kaza ba. Su ma sauran jama’a duk sun kaza, domin a yanzu ta kai kowa ma ya zama mai garkuwa da mutane.
Garkuwa Da Mutane Ya Zama ‘Kasuwancin Samun Kudi’
“Saboda idan ma ba ka yi, to ka san masu yi, amma ba ka iya yin komai a kai. Ko kuma ka san masu yi, sannan kuma da kai ake hada baki, ana yi wa wani ko wasu garkuwa, domin a samu kudi.
“Garkuwa da mutane a yanzu dai kam zan ma iya cewa ta zama ‘wani kasuwancin tara kudi a lokaci daya.’
Dasin, wanda shi ne Dan Majalisar Tarayya da ya wakilci Kananan Hukumomin Fufore da Song daga 2015 zuwa 2019, ya kara da cewa, “ Yanzu mutane sun ma daina damuwa a kan wanda aka kama aka yi garkuwa da shi. Babu ruwan su da kowa ne ne, kowa ce ce, kuma ba su damu da wadanda suka yi garkuwar ko nawa aka biya aka saki wanda aka yi garkuwa da shi din ba.
Garkuwa: An Gudu Ba A Tsira Ba
“ Yanzu masu garkuwa sun shigo da sabuwar dabara. Saboda yawanci a kauyuka maza ba su barci, saboda da sun ji masu garkuwa sun tunkaro, sai su tsere.
“To wadannan masu garkuwa sai suka sake dabara. Idan sun je gidan wani, suka samu ya tsere, sai su kama matar sa ko wasu ’ya’yan sa. Ka ga dai tilas sai ka biya kudi, duk kuwa da cewa ba kai din aka kama ba.
“Kai yanzu fa ta kai ta kawo a kauyukan mu da wahala ma ka samu mai jarin naira 50,000 zaune a kauye. Duk sun gudu, sun koma cikin garuruwa. Domin gudun kada a yi musu takakkiya har gida a sace su.
Da Dan Gari A Kan Ci Gari
Tsohon Dan Majalisar ya bayyana cewa munin abin ya kai gargara, har dan garin ku ko dan uwan ka za a hada baki da shi a yi garkuwa da mutum. Wasu lokuta ma saboda galatsi, masu garkuwar za su fada maka cewa, sai masu garkuwa su ce maka dan uwan ka wane ne ya fada mana cewa ka na da kudi.
Sai dai kuma ya ce ya kamata a yi gaggawar shawo kan lamarin nan, domin idan aka ce za a rika guduwa ko ana yin hijira zuwa cikin garuruwa, to akwai babbar matsala fa a gaba.
Shi kuwa kakakin ‘yan sanda na jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, ya ce jami’an su na bakin kokarin su, kuma suna samun nasara a kan masu garkuwa.
Ya ce a cikin 2019 kadai, sun damke masu garkuwa sama da 300 a jihar Adamawa.