ADAMAWA: Gwamna Fintiri ya yi wa ma’aikata 5,000 ‘korar-kare’

0

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya kori ma’aikata 5,000, ba tare da biyan su ladar zafin zaman rashin aikin yi ba.

Majalisar Zartaswar Jihar ce ta kafa kwamitin da ya bi diddigin ma’aikatan da gwamnatin baya ta APC ta dauka aiki, inda kwamitin ya gano cewa an dauki ma’aikata sama da 5,000 ba bisa ka’idar daukar ma’aikata da gwamnatin Jihar Adamawa ta shimfida ba.

Gwamna Fintiri bai yi wata-wata ba, bayan gabatar masa da rahoton kwamiti, sai ya sa hannun amincewa da korar ta su.

Ranar Laraba, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Adamawa, Umar Pella ne ya yi wannan sanarwa, a Gidan Gwamnati, a Yola, Babban Birnin Jihar.

Pella ya ce duk wani ma’aikacin da ya san an yi masa daukar kwasar-karan-mahaukaciya tsakanin watan Satumba, 2018 da kuma Mayu, 2018, to an sauke shi daga aiki kai-tsaye.

Kwamishina Pella ya ce amma mutum na da damar sake cika fam domin a sake duba daukar sa, idan har ya cancanta.

“Daga yau babu ruwan Gwamnatin Jihar Adamawa da ku, saboda ku ba ma’aikatan jihar ba ne.

Haka nan kuma wannan kora ta shafi dukkan wasu masu mukaman siyasa da gwamnatin APC ta kafa a zamanin tsohon gwamna Bindow.

” Duk wani wanda aka bai wa mukamin siyasa a waccan gwamnatin, to daga ranar 29 Ga Mayu babu ruwan wannan gwamnatin da shi, an soke takarar daukar sa aiki.” Cewar Pella.

Wadanda wannan sanarwa ta shafa, sun hada dukkan kwamishinoni, Shugaban Ma’aikatan wancan lokacin, Manyan Mashawartan Gwamna, Manyan Hadiman Gwamna da sauran su.

Gwamnatin Fintiri ta yi awon-gaba da Shugabannin Hukumar Shari’a ta Jihar Adamawa, Hukumar Kula da Ma’aikata, Hukumar Kula da Harkar Lafiya ta Jihar Adamawa da wasu hukumomi da dama.

PREMIUM TIMES ta gano cewa dama wadanda aka kora din sun kai watanni bakwai ba tare da biyan su albashi ba. Sai a baya-bayan nan ne aka fara raba musu takardun sallama dama aiki.

Share.

game da Author