ADAMAWA: Gumurzun sojoji da Boko Haram a Michika ya tilasta mutane tserewa kan tsaunuka

0

Daruruwan mazauna yankunan karkakar Karamar Hukumar Michika da ke jihar Adamawa sun tsere neman mafaka a kan tsauni, yayin da Boko Haram suka kai musu farmaki.

Majiya ingattacciya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa cikin dare Boko Haram din suka kai farmaki, wanda ya tilasta daruruwan mutane tserewa.

Sun isa yankin wajen karfe shida na yamma, kuma suka shafe sa’o’i su na kai hare-hare.

Majiyar da ita kan ta sai da ta ce ta tsere a kan tsauni, ta shaida wa PREMIUM TIMES a lokacin da ta ke a kan tsaunin cewa, Boko Haram sun kai hari kauyukan Kwuapale da Kwuapa da ke kusa da Michika.

Wata majiya kuma ta ce maharan sun darkaki kauyen Baza, shi ma da ke kusa da Machika, kuma tilas mutane kauyen suka arce domin tsira da rayukan su.

Wani mazaunin Baza ya turo wa PREMIUM TIMES wani bidiyo da ke nuna wadanda ke iya gudu su na gudun tsira zuwa kan tsauni, wasu kusa na fizgar motocin su zuwa Yola.

An kai wannan hari ne a yankunan da akasarin su Kiristoci ne, kuma a lokacin kauyuka sun cika da bakin da suka koma garuruwan su domin bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara.

Gumurzun Sojoji Da Boko Haram

Wani labarin da ya biyo baya kuma, ya nuna cewa an kashe mutane da dama a lokacin da sojoji suka yi kokarin fatattakar Boko Haram daga garuruwan da suka kai wa hari a Karamar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa.

Al’amarin ya faru a ranar Alahamis da daren, wayewar yau Juma’a.

Boko Haram sun kai wannan hari na baya-bayan nan, kwanki uku bayan Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Tukur Buratai ya kai ziyara ga dakarun yaki da Boko Haram, watau Operation Lafiya Dole da ke Madagali, jihar Adamawa.

Tun da farko an sanar cewa Boko Haram sun kai hari a Kopa, Wurogayadi da ke wajen Shuwa da misalin karfe 8 na dare, har mazauna yankunan biyu suka tsere domin ceton rayukan su.

Daga nan sun kutsa Michika har mazauna garin suka tsere zuwa garin Uba, wasu kuwa suka yi mafaka a tsaunukan da ke kewaye da su.

Wadanda suka gani da idon su shun shaida wa Premium Times cewa sojoji tare da taimakon ‘yan bijilanti da ke yanki sun karkashe Boko Haram da dama, wasu kuma sun tsira da raunukan harbi bindiga a jikin su.

” Sun shigo garin Michika daga kauyen Kopa da ke cikin Karamar Hukumar Madagali. Sai suka rabu biyu: wasu suka keta ta cikin Babban Asibitin Michika, wasu kuwa suka nausa cikin garin ta babbar hanyar shiga garin su na harba manyan bindigogi a sama.

” Kafin sojoji su kawo dauki dai Boko Haram sun farfasa wasu kantina, sun saci kaya. Ana haka ne sojoji suka ritsa su da harbi ko ta ina.

“Da ido nan a ga gwarwakin ‘yan Boko Haram sun kai 15 wadanda aka yi fata-fata da su a kan titi.

” Boko Haram sun yi kokarin gudu, amma sai tayar motar su ta yi faci, sai suka diro suka nemi tserewa. Ana sojoji suka rika bindige su.” Cewa majiyar da ta roki a sakaya sunan ta ba sai an bayyana ba.

Wani shugaban al’ummar yankin mai suna Stephen Maduwa, kuma tsohon Shugaban Karamar Hukumar Michika, ya ce jirgin yakin soja ya zo ya rika dankara harbi a kan Boko Haram.

Su kuma mahara sun yi kokarin gudu ta hanyar gangarawa ta kauyen Lassa da ke kusa da Dajin Sambisa.

Kakakin ’Yan Sandan Adamawa, Sulaiman Nguroje ya tabbatar da kai harin da kuma gumurzun. Amma ya ce komai ya lafa.

Share.

game da Author