Da zarar shekarun mutum ya fara haura shekaru 40 a duniya ya zama dole ya maida hankali matuka wajen kulawa da irin abincin da zai rika mua’muala da su, wato ci da sha.
Ga wanda ya shekara 40 ko fiye kula da irin abincin da zai rika ci ya zama dole domin kiwon lafiyar sa.
A shafin ‘THE Healthy’ da ke yanar gizo wata likita mai suna Palinski-Wade ta yi dogon bayani kan irin abincin da ya dace mutum ya rika ci musamman idan shekarun su ya gitta 40.
Domin gujewa fadawa matsaloli na rashin lafiya Palinski-Wade ta lissafo abinci da za a rika yin taka tsan-tsan dasu a lokacin da aka fara haura wadannan shekaru.
1. Naman sa, Rago da Akuya
A lokacin da shekarun mutum suka fara nisa musamma daga shekaru 40 zuwa sama, dole mutum ya rika kaucewa cin nama musamman na S, Akuya da Rago. Duk da suna dauke da sanadarorin dake kara lafiya, a wannan shekaru guje musu shine ya fi dacewa.
A maida hankali wajen cin naman Kaza da kifi suna za su taimaka wa lafiyar mutum idan ya fara zarce wadannan shekaru.
3. Abubuwa masu zaki
Kauracewa abubuwan zaki da suka hada da lemun kwalba, Alawa, chakulet da duk wani abu da ke siga sosai shine abinda yafi dacewa ga mutumin da shekarunsa ya fara zarce 40.
Kamata ya yi a maida hankali wajen cin ‘ya’yan itatuwa kamar su tufa, kankana, ayaba, lemu, abarba da dai sauran su sannan a hada da cin ganyayyaki kamar su ganyen ugu,latas,lansuru da sauran su.
4. Yaji (Barkono)
Yaji ko barkono abu ne da ke kara wa abinci dandano hakan ya sa wasu da dama basa iya cin abinci ba idan babu yaji sosai a ciki ba.
Bincike ya nuna cewa yawan cin yaji musamman ga mai shekaru sama da 40 na kawo masa matsala ga kiwon lafiyarsa. Za a iya kamuwa da ciwon kirji, hawan jini, gyambon ciki da sauran su.
A rika amfani da kayan citta, kaninfari, tafarnuwa, albasa da dai sauran su sun yaji. Sai dai ko da za a ci sai a saka kadan ba da yawa ba.
5. Mai
Kamar yadda aka sani mai kitse ne wanda ake amfani da shi wajen girka abinci iri-iri.
Abin da ya hada da man kuli, kakide, man shanu, bota (Butter) da dai sauran su na cutar da kiwon lafiyar mutum.
Ga mai shekaru sama da 40 kaurace ma shan mai shine mafita. A rika amfani da Mai dan kadan, da kuma man ja ya fi lafiya fiye da man gyada.
Man zaitun na dauke da sinadarin kare zuciyar mutum daga kamuwa da cututtuka,kara karfin ido,hana kiba a jiki da sauran su.
6. Fulawa
Akan yi amfani da fulawa wajen yin cin-cin, cake, buredi, taliya, macaroni da dai sauran su.
Ga wanda shekarun sa ya wuce 40 dole ya rage cin wadannan abinci koda yaushe. A rage cin su a maida hankali wajen cin ganyayyaki da dai dauransu.
7. Soyayyen Abinci
Abincin da aka soya kamar dankalin Hausa da turawa,soyayyen doya,soyayyen nama,soyayyen kwai duk bai dace wanda ya zarce shekara 40 ba ya rika cin su. A rika cin dafaffen abinci ya fi. Ko su din ma za a iya dafa su ne a na ci maimakon haka.
8. Ruwa
Ga dukan mutane yana da matukar mahimmanci a rika yawaita shan ruwa a kowani lokaci ba sai na jira an ji kishi ba.
Shan ruwa na kawar da kamuwa da cutar koda, kawar da ciwon kai, kau da jiri, suma, hana saurin nuna tsufa da dai sauran su.