Abin da ya sa Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare -Zulum

0

Gwamna Jihar Barno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa babbar matsalar rashin yarda da juna tsakanin sojoji da farar hula ce ta sa har yanzu Boko Haram ke mummunar barna a yankin Arewa maso Gabas.

Zulum ya yi wannan jawabi ranar Talata a Abuja, a lokacin da ya ke jawabi a Babbar Kwalejin Tsaro ta Kasa.

Zulum ya kuma kara da bada wani dalilin da ya ce har da rashin kyakkyawan tsarin tunkarar yakin baki dayan sa.

Sannan kuma ya ce cin hanci da rashawa da kuma matsalar yawan dimbin jama’ar da yakin ya kassara, su ma duk babbar matsala ce.

“Sai ka na da abin da za ka iya magance masu ta’addanci za ka iya magance yaki da ta’addanci. Ya kasance ka na da manayan makamai, sauran kayan fada. To amma babbar matsalar a yanzu ita ce rashin amincewa da juna tsakanin sojoji da shugabannin fadar farar hula.

“Wannan kuwa babbar matsala da ta shafi gaba dayan mu, wadda akwai bukatar gaggawa domin an cike wannan gibi da ke tsakanin juna.

“Akwai kuma matsalar cin hanci da rashawa da kuma yawan wadanda hare-haren masu ta’addanci ya tarwatsa daga gidajen su.

“Matsawar ba a maida mutanen da ke tsugune a sansanoni zuwa gidajen ba, to yakin ba zai kare ba. Saboda jama’a za su so kumawa gida su ci gaba da harkokin kasuwanci da sauran sana’o’in da su ke yi.

Daga nan sai ya nemi gwamnatin tarayya ta bijiro shirin gina wa wadanda rikicin ya ritsa da su gidajen su.

Daga nan sai ya kara da cewa shugabancin jama’a musamman a lokacin da ake fada da wasu mahara, to abu ne mai wahala da kuma bukatar amincewar juna da kuma maida hankali sosai.

“Wata matsala dangane da shugabanci ita ce, yadda ba a fada wa shugabannin gaskiya. Sannan su ma shugabannin sun fi son bambadanci, ba su son jin ana fada musu gaskiya.

A jawabin dai na sa na ranar Talaba a wurin taron, ya ce matsalar masu zaman gudun hijira a kai gargara sosai.

“Akwai yara marayu sama da 59,000, kuma akwai zawarawan da sun kai 59,000 su ma.’ Cewar Zulum.

Share.

game da Author