Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB ta bayar da karin haske na dalilin da ya sa dalibar da ta ci maki 302 a Jarabawar shiga jami’a ba a dauke ta a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zari’a ba.
Dalibar mai suna Goodness Shekwobyalo Thomas ‘yar asalin Jihar Neja, ta cika fom na neman shiga Jami’ar ABU domin ta karanta darasin ilmin magunguna.
Rashin daukar ta da aka yi ya haifar da ka-ce-na-ce da surutai a fadin kasar nan ta kafofin soshiyal midiya, inda aka rika caccakar ABU da JAMB baki daya.
“Hujjar da ke gaban mu ta nuna cewa dalibar ce da kan ta ta canja, daga ‘medicine’ wanda ta sa da farko, sai kuma daga baya ta maye gurbin sa da ‘anatomy’.
Wannan canji da ta yi ne ya sa fannin ‘medicine din bai dauke ta ba.
“Da a ce ba ta canja kwas din ba, to da ita ce lamba ta 36 da aka dauka daga cikin dalibai 80 da aka dauka a fannin.
“Bayan da ta canja kwas, sai aka ba ta wanda ta ke so din, kuma ita din ce ma ta dayan da aka fara dauka. Da muka tambaye ta dalilin da ya sa ta canja, sai ta ce mana ai wani ne daga ABU ya kira ta, ya ce ta canja. Mun tambaye ta shaida, amma ta kasa kawo mana. Mun kuma tuntubi ABU, su kuma suka ce ba wanda ya kira ta daga can yace ta canja.
“Amma kuma duk da haka, sai ABU ta ba ta kwas din da ta ke so din, duk da ya ke ba a warware komai a CAPS ba, Sai na tambaye ta me ya sa ba ta shaida wa duniya gaskiyar magana cewa an sauya mata da wanda ta ke so din daga baya ba? Sai ta kasa bayar da wata gamsasshiyar amsa.”
Thomas ta zo ta uku a da maki 288 jarabawar gwaji a cikin daliban asalin jihar Neja, inda Isa Mujahid ya zo na daya da maki 299, sai Hassan Rukayat Nda-Isah ta zo ta biyu da maki 292.
A wurin taron ganawar dai a ofishin JAMB, wakilin Kwamishinan Ilmi na Jihar Neja ya halarta, amma iyayen Thomas ba su je ba, duk kuwa da alkawarin da suka yi cewa za su halarta.
A karshe dai JAMB da ABU sun amince cewa za a dauke ta a fannin da take so din.