Wani dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Kananan Hukumomin Ede ta Arewa/Ede ta Kudu/Egbedore/Ejigbo ya bayyana cewa ya kamata a zabge yawan ’Yan Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.
Bamidele Salam ya ce a gaskiya kasancewa sun kai har 469, to sun yin yawa matuka, kuma kudaden da ake kashewa wajen daukar nauyi da dawainiyar su sun yi yawan gaske.
Daga shawarar da ya bayar, ya ce kamata ya yi a zabge kashi biyu bisa uku, ta yadda za a rika zaben sanata daya tal ya wakilci jiha daya.
Su kuma mambobin Majalisar Tarayya sai a zabge kashi biyu bisa uku na yawan su.
“Mambobin Majalisar Tarayya 360 sun yi yawa.Kamata yayi a zabge kashi 2 bisa 3. Su ma Majalisar Dattawa a rika turo sanata daya tal ya na wakiltar jiha daya, maimakon sanata uku a kowace jiha, komai girman ta kuma komai kankantar ta.”
Honorabul Salam ya kuma bada shawarar Sanatoci su rika yin zaman-wucin-gadi, wato sai ranar da majalisa za ta zauna kadai za su baro garuruwan su, kuma sai ranar da suka zauna kadai za a biya su kudaden alawus na zama kawai.
‘Ministoci 15, Kwamishinoni 7 Sun Wadatar’
Dan Majalisar Tarayya Salam ya ce domin a rage kashe kudaden gwamnati barkatai, kamata ya yi a ce Ministoci ba su wuce 15 ba, a jihohi kuma kada a nada kwamishinoni sama da bakwai.
“Maganar gaskiya ita ce ba mu iya ci gaba da irin tsarin da mu ke a kai, amma a kullum sai ci gaba da tafiya mu ke yi ana yaudarar juna.”
Salam ya yi wadannan bayanai a cikin wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES.
Ya ce shi a ko da yaushe ya na fafutikar ganin an rage karkashe kudaden gwamnati barkatai. Ya kamata a rika sara ana duban bakin gatari.
“Bai kamata kasa kamar Najeriya mai al’umma sama da milyan 200 ba, ta kasance ta na kashe sama da kashi 70 bisa 100 na kasafin kudin ta wajen biyan manyan shigabanni da sauran albashi da alawus-alawus da suka wuce hankalin mai hankali.
Kafin Salam, shi ma Sanata Rochas Okorocha ya taba yin makamancin wannan kira, inda ya nemi a rage Majalisar Tarayya zuwa mambobi da sanatoci daga 469 zuwa 146.