A gina wa masu gudun hijira gidaje, ba sansanoni ba – Zulum

0

Gwamnan Jihar Barno, Babagana Zulum, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira cewa a maida hankali wajen rika gina wa ‘yan gudun hijira gidaje, maimakon gina musu sansanoni da sunan wai matsuguni.

Zulum ya nemi a gina musu gidajen zama na dindindin din ne, inda ya ce maida hankali da ake yi ana gina sansanonin masu gudun hijira ba ya yin wani tasiri wajen ganin an zaunar da su a wurare na dindindin.

Ya ce irin tallafin agajin da ake samu daga kungiyoyin agaji, ba ya yin wani tasiri muddin ba an rika gina wa masu gudun hijira gidajen zama na dindindin ba.

An dai hakkake cewa wannan yaki na Boko Haram da ya shafe sama da shekaru goma ana fafatawa, ya yi sanadiyyar raba akalla mutane milyan biyu daga gidaje da garuruwan su.

Sai Zulum ya ce idan aka rika gina musu gidaje, hakan zai sa su rika tashi daga sansanoni.

Da ya ke jwabi a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira, Lado Mohammed da kuma wakilin ‘Gidauniyar Qatar Foundation’, Zulum ya ce lokaci ya yi da za a rika samarwa masu gudun hijira gidajen zama na dindindin, maimakon a rika yi musu bukkokin a sansani.

Daga nan sai ya ce gwamnatin jihar sa za ta ci gaba da bada goyon baya ga irin wadannan hukumomi domin ci gaba da inganta rayuwa masu gudun hijira, da kuma ganin an shawo kan wannan matsala.

Gwamna Zulum ya yi matukar godiya dangane da irin agajin da hukumar ke bayarwa. Sai dai ya roki ta sauya daga gina sansanoni a koma ana gina musu gidajen komawar su na dindindin.

Share.

game da Author