Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kakkausan kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su daina kallon ta’addancin da Boko Haram ke yi a matsayin wani ‘jihadi’.
Ya ce kamata ya yi ‘yan Najeriya su kara dankon zumunci da hadin kai da juna a wannan lokaci na yaki da ‘yan ta’adda, domin tabbatar da sorewar zaman lafiya a kasar nan.
Buhari ya kara da cewa ‘yan Najeriya su tabbatar sun ki karkata wajen kokarin rabuwar kawuna a tsakanin su, kamar yadda Boko Haram ke ta kokarin ganin sun raba kan jama’a.
Ya ce idan aka mika kai borin Boko Haram ya hau, to bukatar ‘yan ta’addar ta biya kenan.
Ya ce Boko Haram na kokarin ganin cewa sun cusa wa mutane akidar su yadda za ta kawo rabuwar kai a tsakanin jama’a. Ko kuma wasu su rika yi wa wani bangare wannan kallo na mummunar fahimta.
Jawabin Buhari ya biyo bayan wani zargi ne da Kungiyar Kiristoci ta Kasa, CAN ta yi cewa ana musguna wa Kiristoci a kasar nan.
Kungiyar ta yi korafin ne bayan da wani rahoto da kasar Amurka ta fitar ya bayyana cewa ana musguna wa Kiristoci a jihohin Kaduna, Benuwai, Filato, Adamawa da Taraba.
A ranar 26 Ga Disamba, Kungiyar ta’addanci ta IS ta fito da wani faifan bidiyo da aka nuno ta na daukar nauyin kisan wasu Kiristoci 11.
Kungiyar ta ce ta yi hakan ne a matsayin ramuwar gayyar kisan shugaban ta Abu Bakr al-Baghadadi, wanda harin sojan Amurka ya kashe cikin Oktoba.
Masu hangen nesa na ganin cewa an fitar da bidiyon domin a kara ruruta wutar rikicin addini tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya.
Buhari ya y i wannan jawabi ne ta bakin Kakakin Yada Labaran sa, Garba Shehu, wanda ya kara da cewa, “Abu mai muhimmamci ne dai a kasar nan kowa ya san yadda Musulmi da Kiristoci suka hadu wajen yin tir da Boko Haram da kuma dukkan irin mummunan aiki da kisan da suke aikatawa.”
Discussion about this post