2020: Zamu samar wa mutane ayyukan yi a Najeriya – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara jaddada alwashin da ya dauka cewa da za a samarwa mutane ayyukan yi a fadin kasar nan.

Da ya ke jawabin murnar shiga sabuwar shekara ta 2020, Buhari ya ce ya na mai alfahari cewa wannan shekara ce karo na farko a tsawon shekaru da ‘yan Najeriya za su dafa abincin walimar murnar sabuwar shekara, ba tare sun dogara da abincin kasashen waje ba.

Ya yi bayanin cewa zai kara kaimi wajen inganta matakan tattalin arziki, ayyukan raya kasa, tsaro, lantarki da noma, kiwon lafiya da bude kofofin kara yawan danyen fetur da gas da kasar nan ke hakowa.

Buhari kuwa ya jinjina wa wadanda suka yi nasara a zabukan 2019 tare da wadanda suka garzaya kotu domin neman hakki.

Batun ji-ta-ji-tar neman tazarce kuwa, Buhari ya kara tabbatar da cewa ba zai sake neman tsayawa kowane irin zabe ba kasar nan.

Sai dai ya ce zai zama uba daga cikin masu bada shawarar gudanar da sahihin zabe a Najeriya da Afrika ta Yamma baki daya.

Ya yi bayanin yadda za a karfafa tare da inganta tsaro da yakin dakile Boko Haram da sauran bangarorin masu tayar da zaune tsaye a kasar nan.

Shugaba Buhari ya ce rufe kan iyakoki da Najeriya ta yi ya zama dole, idan aka yi la’akari da yadda al’amurra suka sakwarkwace a cikin kasar nan, ta yadda ake shigo da kowane irin tarkace da kuma barazana ga tsaron kasar nan.

Amma kuma ya ce a tuna yadda Najeriya ta rungumi dukkan kasashen da ke makautaka da ita, tamkar ‘yan uwan juna. Ya ce hakan ba zai sa kasar nan ta zura ido ta na samun tawaya daga yadda ake sunkurun haramtattun kayayyaki ta kan iyakokin kasar nan ba.

Ya jinjina nasarorin da aka samu a fannoni da dama, musamman ta fannin noma da tsaro.

Sannan ya ce a karo na farko za a fara amfani da kasafin kudi na sabuwar shekara tun daga watan Janairu da ya kama yau Laraba, farkon sabuwar shekara.

Share.

game da Author