ZAMFARA: Gwamna Matawalle ya yi zargin wasu na shirin hargitsa zaman lafiya a jihar

0

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana cewa wasu marasa kishin jihar na kokarin hargitsa zaman lafiyar da aka samu a karkashin mulkin sa.

Cikin wata takarda a Mashawarcin sa kan Yada Labarai, Zailani Baffa ya sa wa hannu, ta bayyana cewa, wasu na nan sun kammala hargitsa zaman lafiya, ta hanyar shirin shirya zanga-zangar nuna bakin jini ga gwamnati a fadin kananan hukumomi 14 na jihar.

Baffa ya ce manufar marasa kishin shi ne su tunzira mutane a kan gwamnati domin su nuna rashin jin dadin su, duk kuwa da cewa an samu zaman lafiya a jihar.

Zamfara ta sha fama mummunan rikicin makiyaya da manoma, wanda daga baya Fulani suka fantsama garkuwa da mutane da kuma hare-haren banka wa kauyuka wuta.

Tun bayan da Bello Matawalle ya zama gwamna, an samu sauki, ta hanyar cimma yarjejeniyar ajiye makamai da aka cimma da maharan.

Idan ba a manta ba, Cikin watan Nuwamba Matawalle ya zargi tsohon gwamna Abdul’aziz Yari da kokarin haddasa rikici a duk lokacin da ya shiga jihar. Sai dai kuma a wannan karon, gwamnan bai bayyana ko wu wane ke kokarin haddasa barkewar rashin zaman lafiya a jihar ba.

Gwamnan ya yi kira ga jama’a kada su kula masu neman shirya zanga-zanga, domin ba masu kishin zaman lafiyar da aka samu ba ne a Zamfara.

A karshe ya ja kunne cewa gwamnatin sa ba za ta zura ido tq kyale wasu tsiraru su haddasa husumar tashin hankali, bayan zaman lafiya da aka samu a fadin Jihar Zamfara ba.

Share.

game da Author