Gwamnan Jihar Bayelsa mai barin gado, Seriake Dickson, ya yi ikirarin cewa an kashe mambobin jam’iyyar PDP su 12, a zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 16 Ga Nuwamba, wanda aka yi kazamin rikici.
Baya ga wadannan mutane 12 wadanda ya ce duk ‘yan jam’iyyar PDP ne, Dickson ya kara da cewa an guntule kan wasu mutane 10, duk a lokacin wannan zabe.
Dickson ya yi wannan bayani ne a ganawar da ya yi da manema labarai a Abuja.
Ya ce kamar yadda wadanda suka gani da idon su suka tabbatar masa, “an guntule kan mutum 10, aka daddatsa naman jikin su, sannan aka watsa naman su a cikin teku.’’
“Dukkan mutanen da aka kashe din nan, ba wani laifi suka yi ba. Laifin su kawai shi ne su ‘yan PDP ne. Har yanzu kuma ba a ce komai ba dangane da irin cin zarafin jama’a da aka yi a Nembe.
Dickson ya ce yawancin magudin zaben da aka yi wa PDP duk a Nembe, Ijaw ta Kudu, Ogbia da Yenagoa aka yi su.
Gwamnan wanda dan takarar da ya dora zaben gwamna ya fadi, ya zargi jami’an tsaro da wasu jami’an hukumar zabe da hada bakin yin magudi, musamman ta hanyar daukar jami’an zaben da ba bisa ka’ida aka dauke su ba.
”Ba zaben gwamna aka yi a Bayelsa ba, juyin mulkin dimokradiyya ne kawai aka yi. Tuni dama an rigaya an shirya sakamakon zaben ta hanyar daukar jami’an zabe ba bisa ka’ida ba. Aka je Benin aka ba su horo, sannan aka kai mana su aikin zabe a Bayelsa.
“A Nembe tare da sojoji aka yi magudin zabe, har ma da ‘yan bindiga, wadanda suka aka rika dangwala kuri’u, suka dangwala wa APC kuri’u 80,000.
Dickson ya ci gaba da bayyana yadda aka yi magudi a zaben gwamnan Bayelsa, tare da cewa za su ci gaba da neman hakkin su a kotu, domin fashi ne aka yi a Bayelsa, ba zabe ba.
Discussion about this post