Yusuf Buhari ya roki kotu ta kwato masa ‘ya’yan sa da Hadiza ta gudu da su

0

A ranar Juma’a ne wani magidanci mai suna Yusuf Buhari ya roki kotun shari’a dake Magajin Gari a Kaduna da ta kwato masa ‘ya’yan sa da canja musu makaranta bayan ta kwashe su zuwa gidan iyayenta.

Buhari ya bayyana cewa dama can shi ya nemi kotu ta raba wannan aure na su da Hadiza Muhammad amma wata babbar kotu ta hana hakan ya tabbata.

Ya kara da cewa tun bayan haka sai Hadiza ta dauke ‘ya’yan sa ‘yan mata biyu da suka haifa tare ta kai su gidan iyayen ta sannan ta canja musu makaranta. Sannan ta hanani ganin ‘ya’yan.

Buhari dai ya roki kotu da ta tursasa Hadiza da ta dawo masa da ‘ya’yan sa.

Hadiza ta ce ta tafi da ‘ya’yan ne sabida ita ma tana da ikon yin gaka bisa ga karantarwar addinin musulunci.

Alkalin kotun Murtala Nasir ya dage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Disemba sannan ya umurci lauyan Hadiza wato Adam Hassan da ya gabatar da takardun hukuncin da babbar kotun ta yanke kan raba auren da Buhari ya nema ayi a zama mai zuwa.

Share.

game da Author