Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Masar a yau Talata, domin halartar taron Aswan, wanda taro ne domin “Cimma Zaman Lafiya da Ci Gaba Mai Dorewa a Afrika.”
Wannan ne karo na 12 da Buhari zai fita kasashen duniya tun bayan sake rantsar da shi a karo na biyu, a ranar 29 Ga Mayu, 2019.
Taron dai na kwanaki biyu ne, daga 11 zuwa 12 Ga Disamba, 2019, za a tattauna batutuwan da suka shafe dangantakar zaman lafiya da kuma bunkasar ci gaba kasa a Afrika.
Sannan kuma kasashe za su gano hanyoyin da za a bi domin cimma mafita a aikace.
Shugaban Kasar Masar, Abdel Fattah el-Sisi ne zai kaddamar da bude wannan taro, a matsayin sa na Shugaban Kungiyar Kasashen Afrika, AU.
Wannan kuma wata sabuwar ajanda ce ta 2063 da kasashen Afrika za su tsaida domin ganin an cimma nasarar ta magance dimbin matsalolin da ake fuskanta.
Ana sa ran halartar shugabannin kasashen Afrika, shugabannin manyan kungiyoyi da cibiyoyin hada-hadar kudade, manyan ‘yan kasuwa da masu masana’antu, fitattun masana da za su tattauna kalubale da kuma hanyoyin magance su.
Idan za a iya tunawa, tun cikin watan Oktoba ne shugaban Masar ya turo wa Buhari takardar gayyatar sa halartar wannan kasaitaccen taro.
Cikin wadanda za su raka Buhari, har da Gwamnonin Adamawa, na jihar Edo da kuma na Yobe.
Akwai kuma Ministan Tsaro, Bashir Magashi, Babagana Munguno, da kuma Daraktan Jami’an NIA, Ahmed Rufai.
Buhari zai dawo gida Najeriya ranar Juma’a mai zuwa.
Discussion about this post