‘Yan sanda sun kama barayi, mashaya, dilolin muggan kwayoyi a jihar Barno

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Barno ta cafke ‘yan iskan gari da suka addabi mutane 56 a wurare daban-daban a jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda Mohammed Aliyu ya bayyana haka inda ya kara da cewa rundunar ta kama wadannan mutane ne bayan kaimi da rundunar ‘yan sanda ta ‘Operation PUFF ADER’ ta yi a fadin jihar.

Aliyu yace sun kama wadannan mutane da aikata laifukan yin lalata da matan gari, satan shanu, fashi da makami, garkuwa da mutane, fyade, damfara, kisa da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Ya ce a ranar 9 ga watan Disamba rundunar ta damke wani direban babban mota dauke da buhunan ganyen wiwi a Maiduguri.

Direban ya dankara buhunan ganyen wiwin ne a karkashin itacen girki da ya jido a samar motar sa.

Sannan kuma a ranar 22 ga watan Nuwamba ‘yan sanda sun kama wani dan fashi a kusa da rukunin gidaje na Dikwa, da wani kuma baraown wayar hannu a Maiduguri.

“A ranar 4 ga watan Disamba ‘yan sanda sun kama barawon mota a Maiduguri kuma a ranar 7 ga wannan wata aka kama wani dake garkuwa da mutane. Sannan an kama wasu barayin shanu guda uku a kasuwar Kwaya Kusar.

“An kuma kama wasu mutane biyu da laifin yin satifiket din kammala karatun digiri na jami’ar Maiduguri da wani kuma dake badda kama da kayan sojoji.

Bayan haka Aliyu ya ce a Galadima Maiduguri ‘yan sanda sun kama mutane 36 da laifin zina, yin ta’ammali da safaran wiwi.

Ya ce rundunar ta kama mutane shida da laifin fyade, daya da laifin kisa sannan biyu da laifin danfaran mutane.

“An kuma kama wata babbar motar daukan kaya mai lanba DBT 421XA dauke da wiwi, miyagun kwayoyi, janareta da kayan kallo.

Rundunar ta hako wani bidiga kirar Ak 47 wanda Boko Haram suka burne.

Aliyu yace mafi yawan wadannan bata gari matasa ne sannan yayi kira ga iyaye da su rika kula da ‘ya’ayn su da kuma basu tarbiyya na gari.

Share.

game da Author