‘Yan bindiga sun kai hari kusa da gidan Goodluck Jonathan

0

Wani hari da wasu mahara suka kai kusa da gidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a garin Otuoke, jihar Bayelsa, ya ci ran soja daya daga cikin masu gadin gidan.

Kakakin Yada Labarai na Jonathan, mai suna Ikechukwu Eze, ya tabbatar da cewa an kai harin a shingen da sojoji ke binciken masu shiga gidan Jonathan a Otuoke, da ke cikin Jihar Bayelsa.

Eze ya ce kan kashe soja daya, amma daga karshe maharan sun tsere, ganin sun ba su iya jure wa wutar da sojojin suka bude musu.

“Bayan kashe soja daya, sun kuma ji wa wani soja rauni, wanda a yanzu haka ya na asibiti a Yenagoa yana samun kulawa. Zuwa yanzu dai an ce sojan yana samun sauki.”

Eze ya ce lokacin da aka kai harin, Jonathan ba ya gidan.

An dai kai wannan hari ne a jijjifin safiyar Talata.

Tuni Jonathan ya nuna jimami da ta’aziyyar sojan da aka kashe ga iyalan sa. Ya kuma yi alhinin raurnin da aka ji wa daya sojan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kara tsaurara tsaro a gidan da kuma kan hanyar shiga garin Otuoke da nan ne mahaifar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Goodluck Jonathan da jam’iyyar sa ta PDP sun sha shi a hannu APC a zaben da akayi a watan Nuwamba.

Share.

game da Author