A ranar Asabar da ta gabata ne mazauna Maiduguri, babban birnin Jihar Barno suka shiga halin takura, yayin da ‘yan sanda suka datse dukkan manyan titinan garin, saboda bakin manyan jami’an gwamnati da suka halarci bikin ‘ya’yan Shugaban Kamfanin NNPC, Kyari Mele.
Wannan daurin aure na ‘ya’yan Shugaban NNPC dai ya kasance shi ne babban al’amari kuma kasaitaccen taro mafi girma a Maiduguri a cikin shekarar 2019.
Kimanin jiragen sama 46 ne suka sauka Maiduguri a ranar Asabar wadanda suka rika karakainar kai manyan baki zuwa daurin aure a Maiduguri.
PREMIUM TIMES ta binciko cewa kafin daurin auren dai bai fi jirage biyar kacal ne ke sauka a filin jirgin Maiduguri a kowace rana.
Al’ummar Maiduguri sun wayi gari sanyin safiya, sai dai suka ga ‘yan sanda sun kulle dukkan manyan titinan garin, musamman hanyar da ke nufa filin jirgin saman Maiduguri.
Hanyoyin da aka kulle sun yada da Kano Road, wadda aka kulle bangare daya, Sir Kashim Road, sai kuma Dandal zuwa Fadar Shehun Barno.
An kuma kulle hanyar daidai Randabawul da ke Horseman da sauran manyan titina. Dama tun ranar Talata jami’an ‘yan sanda sun bada sanarwar cewa za su kulle titinan garin saboda tsaro.
Sai dai ba su ce ga dalilin yin haka din ba. Babu wanda ya san cewa za a kulle titinan garin ne saboda kare lafiyar manyan jami’an gwamnati da za su je daurin aure.
Dimbin jama’ar da wannan lamari ya kuntata wa sun shiga shafukan su na Facebook su ka rika nuna rashin jin dadi da kuma bacin rai.
Cikin wadanda suka yi kakkausar suka a shafukan Facebook akwai Usman Alkali, Haliru Musa da kuma Habila Mutah.
Mutane da dama sun rika tafiya kasa, sannan kuma sauran titinan da aka bari ana bi sun cunkushe sosai da ababen hawan da aka takure a wasu kebantatrun hanyoyi.
Dama kuma garin Maiduguri a cike ya ke, saboda ba yawaitar masu gudun hijira a garin.
Discussion about this post