Fadar Shugaba Kasa ta jaddada halascin sake kama Omoyele Sowore da jami’an SSS suka yi.
“Sowore ya yi kira a fito a kifar da halastacciyar gwamnatin da aka zaba a turbar dimokradiyya.
“ Ya yi wannan kran a cikin talbijin da kuma a matsayin sa na mashahurin mawallafin kafar yada labarai fitacciya da ya ke yadawa daga Amurka.”
Haka Garba Shehu, Kakakin Yada Labarai a Shugaban kasa ya bayyana cikin wata takardar da ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Daga nan kuma sai Shehu ya ce SSS ba su bukatar jiran umarni daga Shugaban Kasa idan za su wanzar da aikin su, domin akwai yadda doka ta shimfida musu aikin na su.
“ Jami’an DSS ba lallai ba ne sai sun jira umarni daga Shugaban Kasa idan za su gudanar da sha’anin aikin su ta shimfida musu, karewa da tabbatar da dorewar dimokradiyya, tun daga 1999,Sai dai kuma Garba Shehu bai yi magana kan shin ko Shugaba Buhari ne ya bada umarnin a kamo Sowore, wanda shi ma ya yi takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019.
Sama da kwanaki 120 kenan ake tsare da Sowore da kuma Olawale Bakare a ofishin SSS, duk kuwa da kotu na ta bayar da belin su.
An bayar da belin su ranar Laraba da ta gabata, amma kuma washegari Alhamis aka sake kama shi, bayan an yi tirja-tirja a Babbar tirja-tirja a cikin babbar kotun tarayya, Abuja.
Ana tuhumar su biyu da laifukan kokarin shirya makarkashiyar kifar da gwamnati, cin amanar kasa da kuma cin zarafin Shugaba Muhammadu Buhari.
A cikin sanarwar da Garba Shehu ya fitar, ya kamanta kurarin da Sowore ya yi da irin laifin ‘yan Boko Haram.