Yadda APC ta rufe bakin masu neman zuga Buhari yin tazarce a 2019

0

Jam’iyyar APC ta yi barazanar korar masu kiran Shugaba Muhammadu Buhari ya fito takara a zaben 2023.

APC kuma ta kara nesanta kan ta da duk wani batun na tazarce a zaben 2023 tare da kara jaddada cewa Shugaba Buhari na nan a kan bakan sa cewa ba zai sake neman shugabancin kasar nan ba, idan wa’adin mulkin say a cika a 2023.

APC kuma ta yi tir da wani mai suna Charles Enya, wanda ya yi ikirarin cewa a matsayin sa na dan jam’iyyar APC, ya shigar da kara ya na neman a tilasta wa Buhari tare da gwamnoni zarcewa a 2023.

Jam’iyya mai mulki dai ta ce ba da yawun ta Enya, dan asalin jihar Ebonyi ya kai wannan kara kotu ba.

Daga nan kuma APC din har ila yau a ta bakin Kakakin Yada Labaran ta, Lanre Issa-Aremu, ta nanata cewa za ta binciki Enya, idan har ya tabbata mamba ne a jam’iyyar APC, kamar yadda ya yi ikirari, to za ta ladabtar da shi, ta hanyar kora kwata—kwata daga APC.

APC ta ce ta na da yakinin cewa Charles Enya karen-farautar ‘yan adawa ne, suka cinno shi domin ya cinna wutar rudanin siyasa a cikin APC da mulkin da jam’iyyar ke tafiyarwa.

“APC ta karanta bayanai dangane da karar da ka ce Enya ya kai kotu, ya na neman kotu ta amince wa Buhari da gwamnoni su zarce, bayan kammala wa’adin 2023.

“To da farko dai APC ta yi tunanin ta watsar da wannan surutan marasa ma’ana, tunda dai shi Shugaba Buhari ya bayyana cewa doka ba za ta bar shi ba, kuma ba ya sha’awa, ba kuma zai sake neman kuri’ar kowa ba.

“Amma sai muka ga dai gara mu isar da kakkausan gargadi ga wannan mai suna Charles, wanda da ji ka san ba da gumin kan sa ya ke ta wannan badanbadama ba, turo aka yi, domin a haifar da rudani.

“To APC na nan kan bakanta cewa Shugaba Buhari ba zai nema ba, kuma ba ya da sha’awar wucewa, hasali ma, dokar Najeriya zango biyu kadai ta amince shugaba da gwamna su yi a kan mulki.

Daga nan APC ta yi gargadin cewa za ta kori duk wani mamba na jam’iyyar mai neman ya kawo wa jam’iyyar ko mulkin da jam’iyyar gudanarwa kafar-ungulu.

Share.

game da Author