Yadda Abubakar ya kashe Budurwar sa daga rakiya

0

A makon jiya ne Kotu a garin Ilori jihar Kwara ta gurfanar da wani manomi mai suna Abubakar Babato dake da shekaru 20 da ake zargin sa laifin kashe budurwarsa mai suna Azumi Bajida mai shekaru 18.

Lauyan da ya shigar da karar Isaac Yakubu ya ce wannan abin tashin hankali ya auku ne a ranar 16 ga watan Nuwamba a kauyen Danwaya Aderan, Bani.

Yakubu ya ce a wannan rana Babato ya je tadi gidan su Azumi. Bayan sun dan zanta sai suka dunguma tare zuwa gidan sa. Kafin subtafi Azumi ta sanar da iyayenta.

Da dare yayi sai mahaifin Azumi bayan bai ga ta dawo gida ba sai ya bi sawu zuwa gidan su Abubakar.

A hanyarsa ne ya yi kicibus da gawar ‘yar sa a kusa da wani juji gab da gidan saurayin ‘yar sa, wato Abubakar.

Yakubu yace nan da nan Bajida ya nufi ofishin ‘yan sanda domin ya sanar musu.

Nan da nan kuwa ‘yan sandan suka kamo Abubakar. Bayan sun yi zurfin bincike akai ne suka gano cewa shi wannan saurayi ne ya kashe budurwar tasa, wato Azumi.

Alkalin kotun maishari’a Muhammed Ndakene ya daga ci gaba da shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Janairu 2020.

Share.

game da Author