Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana a cikin kakkausan gargadi cewa tulin bashin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ciwowa ido-rufe na daf da durkusar da tattalin arzikin kasar nan.
Da ya ke magana a wurin wani taro a Lagos, ranar Juma’a Obasanjo ya bayyana cewa gwamnatin Buhari na neman jefa Najeriya cikin matsanancin halin da kasar da sauran kasashen Afrika da dama suka shiga cikin shekarun saba’o’i da tamanoni, inda basussuka suka shake wa kasashen wuya, ko hadiyar ruwa ma da kyar suka rika yi.
Ya nuna takaicin cewa yawan bashin da Najeriya ke ciwowa ya zame wa gwamnati alakakai, idan aka yi la’akari da kudaden da take diba duk wata daga kudaden shiga ta na biyan bashi da su.
“Sannan da yake ana yi wa Najeriya wani kallo, masu bada bashi babu ruwan su da yin la’akari da halin da kasar ke ciki, su dai duk karshen wata sai Najeriya ta debi kudi daga kudin shigar da ta samu ta biya wani kaso daga bashin da ta rakito.
Obasanjo ya ce ba wai laifi ba ne a ciwo bashi a yi wa jama’a aiki. Amma kuma ya ce ya kasance ana sara kuma ana duban bakin gatari.
” To ita wannan gwamnatin ta yi dan-karen kaurin suna wajen yayumo bashi ba tare da yin kwakkwaran nazari ko duban abin da ka iya zuwa ya dawo ba.”
Ya nuna rashin jin dadin yadda ake ciwo bashi don yin wani aiki, amma kuma da an fara zai a yi watsi da shi.
Tsohon shugaban wanda ya yi mulkin soja tsakanin 1976 zuwa 1979 da kuma 1999 zuwa 2007, ya yi mamakin yadda Najeriya ta dimauce a halin yanzu, ta yadda kamar yadda ya yi ikirari, har bashi ake ciwowa domin a biya wani bashi da kudin sabon bashin da aka ciwo.
Sai ya tunatar da cewa Buhari ya gaji bashin dala bilyan 10.32 cikin 2015. Amma a yanzu ana bin kasar nan bashin dala bilyan 81.274, wato kusan naira tiriliyan 24.947 kenan.
“Babu kasar da za ta iya fita cikin kunshin katutun matsala muddin ta na kwasar kashi 50 bisa 100 na kudaden shiga a kowane wata ta na biyan bashi da su.” Inji Obasanjo.
Ya ce cikin 2018 Najeriya ta kwashi kashi 60 bisa 100 na kudaden shiga ta biya bashi da su.
Ya ce duk wannan bai isa Najeriya ta shiga taitayin ta ba, sai kuma a yanzu gwamnatin Buhari kenan sake ciwo wani bashi har na dala bilyan 29.6
Obasanjo ya ce za a shiga kaka-naka-yi a duk lokacin da farashin danyen man fetur ya karye warwas.
A karshe ya ce, a yadda Najeriya ta ke a yanzu, babu wanda zai sake yafe ma ta bashi har abada.
Idan ba a manta ba, farkon hawan Obasanjo mulki a 1999, sai da ya yi kokarin da har aka yafe wa Najeriya basussukan bilyoyin daloli da shi Obasanjo ya gada daga gwamnatocin da suka gabace shi.
Discussion about this post