Tsakanin Sarkin Kano da Makiyansa, Ya Allah ka bashi Nasara, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Kamar yadda kuka ji, mun samu labarin wata sabuwar makarkashiya, makirci da sharri da makiyan masarautun mu masu daraja, da masarautar Kano suka shirya, a bisa kokarin da suke yi na ruguza kokarin da iyaye da kakannin mu suka shuka na alkhairi. Yanzu haka sun fito da wata karya, wai wasu kungiyoyi masu zaman kan su (Civil Society Organizations) guda talatin da biyar sun kai koke ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, domin wai a cire Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II daga matsayin sa.

Ya ku bayin Allah, wallahi, dukkan wani mutum mai ilimi, mai hankali, mai hangen nesa, wanda yasan abun da yake yi, yasan cewa wannan karya ce! Domin ko hasidin iza hasada, wallahi yasan da cewa Kanawa suna son Sarkin su, kuma suna tare da shi dari-bisa-dari, kuma suna bakin ciki da abun da wannan Gwamnatin take yi masa na musgunawa!

Su waye wadannan kungiyoyin (CSO) idan ba karya ba? Meye sunan su? Kuma a ina suka fito? Mun sani, Gwamna Ganduje yana iya daukar wasu ‘yan tasha, marasa aikin yi, marasa tarbiyya, wadanda basu san girman manya ba, domin ya biya su suyi masa wannan aiki, kasancewar a kasar nan, akwai wasu irin mutane, wadanda indai har zaka biya su, to komai zasu iya yi maka, kuma komai rashin dacewar sa.

To ko ma dai meye, mu addu’ar mu, da rokon Allah mu har kullun, shine, yaci gaba da kare mutunci da Martabar Masarautun mu da Sarakunan mu daga sharri da makircin miyagu masu kokarin mayar muna da hannun agogo baya, kawai ba don wani abu ba sai don kokarin su na ganin sun musguna wa wani. Amin.

Ya ku ‘yan uwa na masu daraja, masu girma, masu albarka! Ku sani, Allah Subhanahu wa Ta’ala ya shaida muna a cikin littafin sa mai tsarki, wato Alkur’ani, cewa lallai yana da sunaye masu girma, kuma ya umurce mu da mu roke shi da su, kuma yayi muna alkawarin cewa, lallai duk wanda ya roke shi zai amsa masa. Kuma yace duk wanda ba ya rokon sa, zai shiga wutar jahannama yana wulakantacce. Allah yace:

“وَلِلّهِ الأَسْمَاء الْحُسْنَى فَادْعُوهُ بِهَا وَذَرُواْ الَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِي أَسْمَآئِهِ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ.”

“اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ لَهُ الْأَسْمَاء الْحُسْنَى.”

“هُوَ اللَّهُ الْخَالِقُ الْبَارِئُ الْمُصَوِّرُ لَهُ الْأَسْمَاء الْحُسْنَى يُسَبِّحُ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ.”

Don haka, muna rokon ku, ya ku masoyan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, kai da ma duk wani mai kishin Musulunci da arewa baki daya, da cewa don Allah, don Allah, don Allah, gobe idan Allah ya kai mu ranar juma’ah, babbar rana, ranar da Manzon Allah (SAW) ya shaida muna cewa akwai wata sa’a a cikin ta da bawa ba zai gushe ba yana Sallah, yana rokon Allah, face Allah ya biya masa bukatun sa, ya amsa masa addu’ar sa da rokon sa. Muyi kokari mu karanta wadannan addu’o’i, da nufin Allah Subhanahu wa Ta’ala ya kara taimakon Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi, akan dukkanin masu yi masa hasada, da masu kiyayya da shi, da masu kokarin ganin bayan sa, da masu yi masa makirci da kulle-kulle na sharri, a duk inda suke a cikin duniyar nan. Allah ya taimake shi, Allah ya kare shi, Allah ya kara kunyata su, kar Allah ya taba basu nasara wurin rusa abunda iyaye da kakannin mu suka shuka na alkhairi. Allah ya ci gaba da dora shi a kan su, ya ci gaba da daukaka shi a kan su. Allah yasa suyi dana-sanin duk miyagun ayukkan da suke yi a kan sa, amin. Ga Addu’o’in kamar haka:

Ya Allahu ka kara taimakon ka ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, Ya Rahmanu ka kara tausaya masa, Ya Rahimu ka kara jin kan ka a gare shi, Ya Maliku ka kare masa mulkin sa, Ya kuddusu ka kara tsarkake shi daga dukkan abun ki, Ya Salamu ka kara masa kwanciyar hankali, Ya Muminu ka kara amintar da shi ga dukkan bayin ka, Ya Muhaiminu ka kara masa kwarjini a idon bayin ka, Ya Azizu ka sa ya rinjayi dukkan magautan sa, Ya Jabbaru kasa yafi karfin duk wani makiri, Ya Mutakabbiru ka kara masa girma da daukaka, Ya Haliku ka kara wa rayuwar sa albarka, Ya Bari’u ka kara masa nisan kwanakki masu albarka, Ya Musawwiru ka kara masa martaba da muhibbah, Ya Gaffaru ka gafarta kura-kuren sa shi da magabatan sa, Ya Qahharu kasa yayi rinjaye akan dukkan mai adawa da shi, Ya Wahhabu ka kara masa kyautar dimbin masoya, Ya Razzaku ka kara yalwata masa, Ya Fattahu ka kara masa budi na alkhairi a duk inda yake, Ya Alimu ka kara albarka a ilimin sa, Ya Kabiru ka kara masa girma, Ya Basidu ka kara yalwata masa, Ya Rafi’u ka kara daga darajar sa, Ya Mu’izzu ka kara daga shi sama, Ya Muzillu ka kaskantar da makiyan sa, Ya Sami’u kasa duniya ta kara jin sa, ji na alkhairi, Ya Basiru ka kara nuna shi duniya ta kara sanin sa, sani na alkhairi, Ya Hakamu ka hukunta mahassadan sa, hukunci mai tsanani, Ya Adalu ka kara masa adalci, Ya Ladifu ka kara tausaya masa, Ya Khabiru ka kara wa Mai Martaba Sarki sani mai amfani, Ya Halimu ka kara masa hakuri da jajircewa, Ya Azimu ka kara girmama shi, Ya Gafuru ka gafarta wa magabatan sa, Ya Shakuru kasa ya kara godewa ni’imomin da kayi masa, Ya Aliyu ka kara masa daraja da daukaka, Ya Kabiru ka girmama dukkanin masoyan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, Ya Hafiyu ka sanyaya masa, Ya Mukitu ka daukar wa Mai Martaba Sarkin Kano fansa akan dukkanin masu bin sa da sharri, Ya Hasibu ka saukaka masa a wurin hisabi, Ya Jalilu ka kara girmama shi, Ya Karimu ka kara masa karimci a wurin bayin ka, Ya Rakibu ka kara masa kusanci zuwa ga re ka, Ya Mujibu ka amsa dukkan addu’o’in mu, Ya Wasi’u ka kara yalwata masa duniya da lahira, Ya Wadudu kasa bayin ka su kaunace shi, Ya Hakimu ka kara masa sani da hikimah, Ya Majidu ka girmama sha’anin sa, Ya Ba’isu ka buda masa hanyoyin alkhairi, Ya Shahidu kasa duniya ta shaida adalcin sa, Ya Haqqu ka kara dora shi akan tafarkin gaskiya, Ya wakilu ka zama wakili a cikin dukkan al’amurran Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, Ya Qawiyyu ka kara masa karfi da girma, Ya Matinu ka kara karfafa sha’anin sa, Ya Waliyyu ka kara masa yawan masoya a fadin duniya, Ya Hamidu kasa shi ya kara zama mai godewa ni’imomin ka, Ya Muhsiy kasa ya gama da duniyar nan lafiya, Ya Mubdi’u kasa ya gama lafiya da mai babban daki, Ya Mu’idu ka kara masa juriya, Ya Mumitu ka halaka makiyan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, Ya Hayyu ka gajiyar da mahassadan sa, Ya Qayyumu ka turmusa hancin magautan sa a kasa, Ya Wajidu kasa su kunyata duniya da lahira, Ya Majidu kar ka biya masu bukatun su, Ya Wahidu kasa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya zamar masu ciwon ido sai hakuri, Ya Ahadu ka rusa duk wani mugun shiri da mugun tanadin su, Ya Samadu ka biya dukkanin bukatun Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, Ya Qadiru ka kuru-ruta al’amarin sa, Ya Muqtadiru ka kara daga kima da darajar sa duniya da lahira, Ya Maqaddimu kasa hannu a cikin al’amurran sa, Ya Mu’akhkhiru ka tsawaita rayuwar sa akan ayukkan alkhairi, Ya Auwalu ka kara rufa masa asiri, Ya Akhiru ka ja kwanan sa akan alkhairi, Ya Zahiru ka sanyaya idanun sa, Ya Badinu ka kara buda masa, Ya Waliyyu ka kara agaza masa, Ya Muta’ali ka kara dafa masa, Ya Barru ka kara albarka a cikin zuri’ar sa, Ya Tawwabu ka karbi tuban sa, Ya Muntaqimu ka kara sa yayi rinjaye akan makiyan sa, Ya Afuwwu ka kara masa afuwa, Ya Ra’ufu ka kara tausayin ka, da rahamar ka, da jin kan ka, ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, Ya Malikal-Mulki ka kara daukaka mulkin sa da masarautar Kano baki daya, da masarautun mu na arewa, Ya Zal Jalali Wal Ikrami ka kara daraja, daukaka da mutunci ga dukkan Sarakunan mu da masarautun mu na Musulunci, Ya Muqsidu ka kara kunyata dukkan wadanda basu yiwa Mai Martaba Sarki adalci, Ya Jaami’u ka kara hada kan bayin ka akan yiwa Sarkin Kano adalci, Ya Ganiyu ka karawa Mai Martaba wadata, Ya Mugni ka kara masa hakuri, lafiya, juriya da imani, Ya Mani’u ka hanawa makiyan Sarki kwanciyar hankali, Ya Darru ka hada su da cutar mantuwa, Ya Nafi’u kar kasa makiyan Mai Martaba su amfani rayuwar su, Ya Nuru ka kara haske a cikin dukkan sha’anin Mai Martaba, Ya Hadi ka kara dora Mai Martaba Sarki a tafarkin da ka yarda da shi, Ya Badi’u ka kara masa rufin asiri, Ya Baki ka kara masa hakuri, Ya Warisu kasa ya samu masu gadon sa a cikin zuri’ar sa, Ya Rashidu ka kara shirya shi domin tunkarar kalubalen rayuwa, Ya Saburu ka kara hakurtar da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II akan zaluncin makiya, kuma ka kara dora shi yaci gaba da cin nasara a kan su, amin Ya Rabbi!

Ya Allahu, Ya Rahmanu, Ya Zal Jalali wal Ikrami, mun roke ka da wadannan Sunaye naka kyawawa, wadanda kace mu roke ka da su, Ya Allah don tsarkin Sunayen ka, don so da kaunar mu ga Manzon ka (SAW), ka tsayawa Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da tsayawar ka. Ka isar masa da isar ka. Ya Allahu muna rokon ka, kayi masa maganin dukkanin masu zaluntar sa, Ya Allah kayi gaggawar kwato masa hakkin sa, da na masarautar Kano, da na talakawan Kano, da na arewa, da Musulmin Najeriya baki daya, amin!

Wassalamu Alaikum

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a same shi a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author