Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi wanda da ne ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya yi mulki 1855 zuwa 1883. Mulkin sa ya kasaita a tsawon shekaru 28 da ya shafe a karagar mulkin Kano, saboda hamshakan ‘ya’yan sa biyar da ke rike da manyan mukamai na sarautu.
Bayan rasuwar Abdullahi Maje Karofi, sai aka nada kanin sa Muhammadu Bello a matsayin Sarkin Kano cikin 1883. Ganin cewa kanin mahaifin su ne aka nada, sai manyan ‘ya’yan Sarki Abdullahi Maje Karofi ba su yi wata tankiya sosai ba.
Yayin da Sarkin Kano Muhammadu Bello ya zauna daram kan mulki, sai ya saisaita dan sa Tukur a matsayin mai jiran gadon mulki, inda tashin farko ya nada shi Galadiman Kano.
Galadima Tukur ya samu shiga a wurin Sarkin Musulmi Adul-Rahman Danyen Kasko domin shi mahaifin sa Sarki Muhammadu Bello ke turawa Sakkwato ya na kai gaisuwa tare da kai manyan kyaututtuka ga Sarkin Musulmi.
Shekara biyu bayan hawan Abdul-Rahman sarautar Sarkin Musulmi, cikin 1893, sai ya nemi gangamin Sarkunan Daular Musulunci domin ya kai wa Argungu hari, ya dakile Kabawa. Satakuna sun amsa kira, amma daba baya ba su shiga yakin ba, domin a tunanin su, ko an tara ganima, ba da su za a raba ba.
Galadiman Kano Tukur ne kadai ya shiga yaki ya taya Sarkin Musulmi yaki da Kabawan Argungu. A lokacin Sarkin Kano dan sa Tukur ya tura matsayin shugaban tawagar dakarun Kano.
Duk da cewa Kabawan Argungu sun fatattaki rundunar Sarkin Musulmi, wadda rundunar Kano a karkashin Galadima Tukur ke ciki, sai Sarkin Musulmi ya rike Tukur hannu biyu.
Ba a dade da gama wannan yakin ba, sai Sarki Muhammadu Bello ya rasu, a cikin 1993. Nan da nan sai Sarkin Musulmi ya umarci Waziri cewa ya nada Galadima Tukur matsayin Sarkin Kano. Nan take dukkan ‘ya’yan Ssrki Abdullahi Maje-Karofi sai su ka ki amincewa. Ana nada Tukur Sarkin Kano, sai suka fice daga Kano, suka nausa Gabas, suka yi sansani. Domin a son su, sarauta ta koma gidan su, a nada yayan su Yusuf.
Daga nan fa Masarautar Kano ta dare gida biyu, da masu goyon bayan sabon Sarki Tukur da kuma masu goyon bayan su Yusuf da Aliyu da Abbas, ‘ya’yan Sarki Abdullahi Maje-Karofi, wa ga Sarki Muhammadu Bello.
Yusuf da Ali da Abbas suka nemi gudummawar Sarakunan da ba su shiri da Sarkin Musulmi, kamar Damagaram, Gumel da Ningi. Sannan kuma suka samu dimbin magoya baya daga cikin kwaryar Kano da sauran garuruwan da ke karkashin Masarautar Kano.
Wasu tsitaru daga Hadeja suka nuna goyon baya ga Sarki Tukur, amma dakarun Yusufawa suka murkushe su.
Sarkin Musulmi ya nemi Sarkin Kwantagora Ibrahim dan Umaru Nagwamatse ya kai wa Sarki Tukur dauki, amma sai ya ce shi ba zai yi yaki da dan’uwan sa musulmi ba.
Dakarun tawaye su ka darkaki Kano, a rika yi gumurzun karo da sokekeniya da bugayya a wajen ganuwa da cikin Kano.
A cikin Kano kuwa, duk wanda aka kama daga bangaren Yusufawa, sai Sarki Tukur ya sa a fille masa kai, ya na kiran su “arna”.
Shugaban tawaye Yusuf ya rasu a sansanin su, sai kanin sa wanda suke uba daya ya hau jagorancin runduna. Bayan wata biyu, suka sake darkakar Kano da yaki, har dai Sarki Tukur ya fice, ya nufi kasar Katsina.
Sarkin Katsina na lokacin ya fusata, ya tura runduna, amma Yusufawa suka murkushe ta. Ba a dade ba aka yi galaba kan Kano, Abbas kanin Aliyu ya kashe Sarki Tukur, wanda mahaifin sa Sarki Muhammadu Bello, kanin mahaifin su Sarki Abdullahi Maje-Karofi ne.
Aliyu, wanda aka fi sani da Aliyu ya hau sarautar Kano cikin 1894, bayan sun kashe dan uwan su Sarki Tukur. Ya yi sarauta har zuwa 1903, lokacin da Turawan mulki suka kwace Kano, shi kuma aka kama shi, aka tsare a Lokaja.
Siyasar raba kan Gidan Sarautar Kano da Gwamna Abdullahi Ganduje ya bijiro da ita, ko shakka babu ta raba kan jihar Kano gaba daya, ba ma Gidan Dabo kadai ba. A Kano ko dai mutum ya na goyon bayan dukkan abin da Ganduje ke yi, ko kuma ya na goyon bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Dukkan keta martabar Sarki da Gwamna ke yi, ba shi ne farau ba. A zamanin marigayi Sardauna Ahmadu Bello, an tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, aka tura shi gudun hijira a Azare, jihar Bauchi. Sai bayan ya shafe shekaru masu yawa a can ne aka dawo da shi Wudil, kuwa da Kano.
Bayan shi kuma, Masarautar Kano a karkashin marigayi Ado Bayero, ta ga wulakanci da tozarci da cin mutumci a karkashin marigayi Gwamnan Kano Abubakar Rimi.
Babu irin hakurin da Sarki Ado bai yi da irin muzantawar da Rimi ya rike yi masa ba. Har dakatar da shi daga fita Kano da kasashen wake sai da Rimi ya yi.
A yanzu da gwamnatin Ganduje ta dauko salo wanda ya fi na Rimi muni, ya rage ga Ganduje ya tuna cewa daga nan da shekaru uku, har abada ba zai sake mulkin Jihar Kano ba.