Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan Najeriya, ya ku ‘yan arewa, ya ku Kanawa masu albarka, kamar yadda kuka sani ne, kuma kuke da masaniyar cewa wasu manyan mu, kuma dattawa masu daraja, karkashin jagorancin Mai girma tsohon shugaban kasar Najeriya, wato Alhaji Abdussalam Abubakar, a bisa amincewa da yardar fadar mai girma shugaban kasar Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari, da kuma kungiyar dattawan arewa masu daraja (Northern Elders Forum), sun sa baki a cikin wannan rikici da gwamnatin jihar Kano take yi da Masarautar Kano, domin kokarin yin sulhu da sasantawa, kasancewar wannan shine zai sa a samu zaman lafiya mai dorewa tare da kaucewa fitina da tashe-tashen hankula a Jihar Kano da ma yankin arewa baki daya.

Sanadiyyar wannan sa baki da manyan mu suka yi, sai muka yi kira ga dukkanin masoya Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, a duk inda suke, da cewa su kame bakunan su da alkalumman su daga maganganu da yin rubuce-rubucen da za su kawo cikas ga wannan tattaunawa da sulhu, domin kuma nuna girmamawa ga wadannan manya namu, wato wadannan bayin Allah, dattijan kirki, tare kuma da nuna da’a da biyayya ga Allah Subhanahu wa Ta’ala da Manzon sa (SAW), a bisa umurnin da suka yi da ayi sulhu, inda har Allah Madaukaki ya nuna cewa, yin sulhun shine yafi alkhairi, da kasancewar Manzon Allah (SAW) ya sulhunta mabiyan sa a wurare daban-daban, kai ba ma Musulmi ba, hatta wadanda ba Musulmi ba, Annabi (SAW) yayi sulhu da su, kamar yadda za mu ga hakan a cikin tarihin rayuwar sa, da ma sulhun hudaibiyyah da yayi da kafirai, mushirikan Makkah.
Duk duba da wannan yasa muka yi kira ga masoyan Sarki da su mayar da wukar su cikin kube, kuma alhamdulillah, sun amsa wannan kira, sun yi da’a da biyayya, suka kame bakin su, suka daina cewa komai, don dama su masu da’a ne da biyayya, sannan masu girmama manya ne tare da ganin kimar su da kuma darajar su!
Munyi zato da tsammanin cewa kamar yadda muka yi haka, saboda samun zaman lafiya tsakanin wadannan shugabanni, da kuma ci gaban Jihar Kano da arewa, su ma magoyan bayan gwamna Ganduje za su yi shiru su daina yin rubuce-rubucen batanci da cin mutunci ga wannan bawan Allah, damo Sarkin hakuri, wato Mai Martaba Sarki, amma sai dai kash, sai muka ga cewa basu daina ba. Sun ci gaba da rubuce-rubucen su na zagi, cin mutunci, habaici, shagube da sauran su.
Wallahi duk mai bibiyar shafukan su Fa’izu Alfindiki da Salihu Tanko Yakasai da sauran karnukan farautar ‘yan siyasar gwamnatin Ganduje a Facebook da sauran kafafen yada labarai na soshiyal midiya, zai ga wannan. Domin Allah shine shaida, ba zamu yiwa kowa sharri, kazafi da karya ba. Domin mun yi imani da cewa, zamu tsaya a gaban Allah domin amsa tambayoyi akan duk abunda muka fada ko muka rubuta!
Ko jiya ma Alfindiki yayi wani rubutu na sharri da karya, mai taken: ‘SARKIN CIKIN GARI SUNUSI YA HANA MASOYIN GANDUJE KUMA MASOYIN CI GABAN JAHAR KANO SHIGA FADAR SA HAR ABADA.’ A cikin wannan rubutu, ya sharara karairayin sa, ya fadi shirme, soki-burutsu da sauran su.
Ina roko, don Allah, manyan mu da suka sa baki cikin wannan rigima, don ayi sulhu, da kar su ga kamar mun raina su, a’a, wallahi sam ba haka bane. Allah ya sani muna ganin girman su da kimar su matuka. Kawai dai nayi wannan rubutu ne domin bayyanawa duniya gaskiyar abun da ya faru game da sallamar Sokon Kano daga fada. Domin yin shiru shi zai sa wadanda basu san me yake faruwa ba su rikice. Kuma yin shiru zai taimaka wa shaidan da mutanen sa azzalumai su samu nasara akan karairayi da sharri da kazafin da suke yadawa don su ci mutuncin masarautar Kano mai daraja. Wanda da ikon Allah har abada ba za su yi nasara wurin kokarin su na farraka zuri’ar gidan Dabo ba! Allah zai ci gaba da kare wannan zuri’a mai albarka duk da cewa wasu miyagun ‘yan siyasa sun yi nasarar saye wasu daga cikin ‘ya ‘yan zuri’ar, sun yarda a rusa wahalar da iyayen su da kakannin su suka sha, akan dan wani abun duniya mai karewa!
Ya ku al’ummah, gaskiyar abun da ya faru shine: ranar da aka yi bikin yaye hafsoshin jami’an ‘yan sanda a Wudil, kowa dai yasan cewa Sokon Kano, Alhaji Ahmadu Abdulwahab yaron Mai Martaba Sarkin Kano ne kuma marokin sa ne. Kuma abunda ake sa rai da tsammani ga dukkanin wadanda suke aiki a wannan fada mai daraja, shine, yin biyayya da da’a da kuma nuna kauna ta tsakani da Allah ga Mai Martaba Sarki, tare da kokarin kiyaye dokokin wannan fada, da kare martabar ta, abunda bature yake kira da LOYALTY. Allah ya sani, babu wani shugaba daga cikin shugabanni, na siyasa ne, ko na addini, ko na sarauta, da zai yarda da yi masa zagon kasa. Wato mutun yana karkashin sa, yana yi masa aiki, yana amfana da shi, amma a wayi gari wannan mutun yana nuna da’ar sa da biyayyar sa ga wani mutun daban. Kuma musamman ace yana biyayya ga wanda yasan cewa makiyin maigidan sa ne. Kun ga, a gaskiyar magana, ba wanda zai yarda da wannan!
Ranar da aka yi wannan biki a Wudil, kawai Sokon Kano, Alhaji Ahmadu Abdulwahab ya tafi yana yin kirari ga Wambai, wato Aminu Ado, kuma yana sukar Mai Martaba Sarki. Ni na san indai har gaskiya muke nema, to kowa yasan ba shugaban da zai yarda da wannan sam-sam, ko waye shi. Sai fa idan zamu bar gaskiya ne mubi son zuciyar mu, to sai muce wannan kuma daban.
A lokacin da aka yi wannan, bayan an dawo gida sai shugaban ma’aikatan fadar Mai Martaba Sarkin Kano, wato Mai girma Danburam Kano, Alhaji Munir Sanusi ya bayar da umurnin sallamar Sokon na Kano. Kuma wallahi, ina mai rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, a lokacin duk da aka yi wannan, Mai Martaba Sarki bai sani ba, baya da labari. Kawai dai su Mai girma Danburam sun dauki wannan matakin da ya dace ne saboda kokarin da suke yi na kare masarautar Kano da zuri’ar gidan Dabo baki daya daga dukkan wani nau’i na cin mutunci, munafurci da wulakanci. Wanda wallahi sai daga baya ne aka yiwa Mai Martaba Sarki bayani kuma ya gamsu, saboda ya ga an dauki matakin daya dace na kakkabe bata-gari daga wannan fada mai daraja!
Ya ku jama’ah, kun ga tsakani da Allah, a cikin wannan sha’ani babu maganar cewa an kori masoyin gwamna ko kuma mai son ci gaban Jihar Kano. Amma shedanu, miyagu, masu kokarin haddasa fitina da kara rura wutar rikici, wadanda suka mayar da wannan rikici hanyar cin abincin su, sun yi rubuce-rubuce na karya cewa wai an sallami Sokon Kano ne don yana son gwamna kuma yana son ci gaban Jihar Kano. Wai har wannan shedanin ya rubuta cewa wannan shine mutun na uku da Sarki ya kora, ba domin komai ba sai don alakar su da soyayyar su ga gwamna Ganduje. Yace an kori Isa pilot, an kori Maja Sirdi, sannan yanzu ga Sokon Kano. Wanda alhamdulillahi, muna godiya ga Allah Subhanahu wa Ta’ala har kullun, da yasa al’ummah suka san da cewa me yasa aka sallami Isa pilot da Maja Sirdi daga fada. Kowa yasan cewa, tun daga kan shugaban kasa har gwamna, kai har kowane shugaba ne, babu wanda zai taba yarda da munafuki, mai yi masa sharri da zagon kasa ba a kusa da shi. Sai fa idan munafukai zamu zama, mu bar hanyar gaskiya!
Saboda haka wannan shine ainihin abunda ya faru. Don haka muna kira ga dukkanin masoya Mai Martaba Sarki, da dukkanin wani mai kaunar zaman lafiya da ci gaba ya san da wannan. Duk wata karya da sharri da kazafi da munafunci da wasu zasu yada, sam ba haka abun yake ba, tatsuniyar su ce kawai.
Shi dai Mai Martaba Sarki, wallahi har kullun shi na kowa ne. Bashi da wani mutun da ya kullata a zuciyar sa. Baya nufin kowa da sharri sai alkhairi. Kuma shi masoyin talakawa ne, mai son ci gaban Musulunci ne da Musulmi, mai son ci gaban Jihar Kano ne da arewa da ma Najeriya baki daya. Sannan uwa uba shi mutun ne mai hakuri, mai kaunar zaman lafiya da kokarin kauce wa dukkanin hayaniya da tashin hankali. Har kullun, duk wanda ke kusa da shi zai ji shi yana yawan cewa, duk abunda ke faruwa ayi hakuri, In Shaa Allahu Allah zai kawo karshen komai. Yanzu ‘yan uwa, don girman Allah, wanda yake haka, wai shine wasu shedanu, miyagu za su sa wa karan tsana, ba don komai ba sai don saboda hassada! To da yardar Allah, Allah ba zai taba basu nasara ba!
Allah yasa mu dace, amin.
Nagode,
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lamba kamar haka: 08038289761.