TAKUNKUMI: ‘Yan jarida 250 aka kulle a 2019

0

Tsarin mulkin kama-karya, matsalar rashin kyakkyawan shugabanci da kuma rfantsamar yawaitar zanga-zanga a Gabas ta tsakiya ya kara haddasa yawaitar daure ‘yan jarida, musamman a Daudi Arabiya, wadda a yau har ma ta fi kasar Masar yin kaurin suna wajen daure ‘yan jarida a duniya.

Kwamitin Kare Hakkin ’Yan Jarida na Duniya CPJ, ya fitar da sakamakon binciken sa na karshen 2019, inda ya fitar da kididdigar cewa a cikin wannan shekara hukumomin tsaro sun garkame ‘yan jarida har 250 a duniya.

Za a iya kunawa cewa cikin 2017 an daure 255,yayin da a 2018aka daure har 273.

An kuma bayyana kasahsen China, Turkey, Saudi Arabia, da Egypt ne aka fi nuna wa ‘yan jarida mulkin kama-karya wajen kokarin hana su gudanar da aikin su.

Akwai kuma kasashen Eritrea, Vietnam da Iran inda aka fi yi wa ‘yan jarida daurin-huhun goro.

Da yawan wadannan ‘yan jarida dai ana zargin su ba ne da laifin yi wa kasar su zagon-kasa, wasu kuma ana tuhumar su da rubuta labarai na kage.

Wadanda ake yi wa irin wadannan tuhume-tuhume dai sun kais u 30. Amma kuma shekarar 2018 guda 28 ne aka yi wa irin wannan tuhuma.

Shekaru hudu baya a jere duk kasar Turkiyya c eke zuwa ta daya wajen danne ‘yancin dan jarida, sai a wannan karon ne aka samu sassauci. Sai dai har yanzu ‘yan jaridar kasar har yau su na mafa da takurawar da aka saba yi musu.

A bana an tsare ‘yan jarida 47 a Turkiyya, a bara kuwa an tsare 68.
An fara wannan binciken ‘yan jaridar da ake daurewa ne tun cikin 1990.

A nan Najeriya ana tsare da wasu, ciki har Agba Jalingo da mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ko da ya ke shi ba a dalilin rubutu a jarida ne ake tsare da shi ba.

Share.

game da Author